Tashin Hankali Yayin da Wani Gini a Cikin Barikin ’Yan Sanda Ya Ruguje a Jihar Oyo
- Yanzu muke samun mummunan labarin yadda gibi ya ruguje a jihar Oyo da ke Kudu maso Yammacin Najeriya
- Rahoto ya bayyana cewa, ana fargabar mutane da yawa sun mutu, kuma a halin yanzu akwai wadanda suka makale a ciki
- Ba wannan ne karon farko da gini ke rugujewa ba a Najeriya, hakan ya zama ruwan dare a wannan lokacin
Jihar Oyo - Ana fargabar mutane da yawa sun mutu yayin da wasu suka makale a cikin wani ginin da ya ruguje a cikin barikin ‘yan sanda da ke Sango a birnin Ibadan na jihar Oyo.
Ginin da ya rugujen an ce yana gaban wani katafaren gidan sama mai hawa uku ne da ke yankin, rahoton The Nation.
Wata majiya ta hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta tabbatar da aukuwar lamarin.
An tabbatar da faruwar lamarin
Majiyar ta shaida cewa, an sanar da hukumar ne da misalin karfe 8 na dare, kuma ta ce tuni aka gayyato jami’an kwana-kwana zuwa wurin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Majiyar ta kuma tabbatar da cewa, akwai mutanen da suka makale a karkashin ginin yayin da ake fargabar da yawa sun mutu.
Daraktan ayyuka na hukumar kwana-kwana ta jihar Oyo, Ismail Adeleke ya ce, ba a sanar dashi halin da ake ciki ba, rahoton Vanguard.
An yi kokarin jin ta baki rundunar ‘yan sandan jihar, amma ba a samu damar hakan ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
An tura wa kakakin rundunar ‘yan sandan jihar sakon tes bai dawo dashi ba, kana an kira shi a waya ba a same shi ba.
Yadda lamarin ya faru
Wasu majiyoyin yankin sun bayyana cewa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 6 na yammacin yau Asabar 22 Afirilu, 2023.
An Ga Tashin Hankali Yan Bindiga Sun Budewa Yan Sanda 5 Wuta Yayin Da Suke Tsakar Cin Abinci A Ranar Idi A Imo
Sun kuma bayyana cewa, jim akdan bayan faruwar lamarin mazauna yankin suka fito don aikin ceton wadanda suka makale.
Sai dai, an ce ba a samu nasarar ceto kowa ba sakamakon tsoron da ake na ci gaba da rugujewar ginin ba zato ba tsammani.
A makon jiya ne wani gini ya danne ma'aikata a wani yankin babban birnin tarayya, inda ake zargin ya kashe mutane masu yawa a lokacin.
Asali: Legit.ng