Lafiyar Tinubu Lau, Babu Jinyar da Yake Ji, Sanata Orji Kalu Ya Yi Magana Mai Daukar Hankali
- Sanata Orji Uzor Kalu ya bayyana yanayin da Bola Ahmad Tinubu yake idan ana maganar lafiyarsa
- Ya bayyana cewa, Tinubu ba a kwance yake a asibiti ba, don haka lafiyarsa kalau sabanin jita-jitan jama’a
- Ana ci gaba da yada jita-jita bayan da Tinubu ya bace bat game da lafiyarsa da kuma inda ya shiga
FCT, Abuja - Ana ci gaba da cece-kuce game da lafiyar zababben shugaban kasan Najeriya, Bola Ahmad Tinubu, inda ake cewa a halin yanzu yana karbar kulawar asibiti.
Sai dai, sanata Orji Uzor Kalu ya yi watsi da duk wata jita-jita da ake yadawa, inda yace lafiyar Tinubu lau kuma ba a kwance yake a gadon asibiti ba.
Kalu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi abikin cikarsa shekaru 63 a Abuja, kamar yadda Tribune Online ta ruwaito.
Bayanan da Kalu ya yi game da lafiyar Tinubu
A cewarsa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Zababben shugaban kasanmu lafiyarsa kalau. Ba gaskiya bane cewa bashi da lafiya. Bana son magana da yawa. Yana cikin koshin lafiya; yana cikin taitayinsa.”
Hakazalika, ya tuna da wata tattaunawa da ya yi da wani abokinsa game da lafiyar Bola Tinubu, Daily Post ta ruwaito.
Ya kara da cewa:
“Wani abokin aiki na jiya ya ce ya ji labarin wai zababben shugaban kasa Tinubu na kwance a asibiti.
“Na shaida lafiyar shugaban kasa mai jiran gado kalau ba ya kwance a asibiti; ba gaskiya bane cewa yana kwance a asibiti. Mun yi musu. Na fada masa zababben shugaban kasa lafiyarsa lau.”
Yadda aka fara yada jita-jita game da Tinubu
A ranar 22 ga watan Mayun 2023 ne aka fara yada labarin jita-jita cewa Tinubu ya fece kasar waje domin neman magani a rashin lafiyar da yake fama dashi.
29 Ga Watan Mayu: Fitattun Yan Najeriya 5 Da Ake Ganin Su Buhari Ke Baiwa Hakuri a Sakonsa Na Barka Da Sallah
Ana zargin cewa, Tinubu ya kwanta rashin lafiya bayan shafe watanni yana kamfen din takarar shugaban kasa a shekarar nan.
Sai dai, tawagarsa ta yada labarai ta gaggauta yin watsi da rahotannin, inda suka ce Tinubun ya tafi Landan da Faris ne domin shakatawa da hutawa.
A bangare guda, shugaban kasa Ukraine ya taya Tinubu murnar lashe zabe, kana ya gayyace shi zuwa kasarsa domin tattauna wasu bayanai.
Asali: Legit.ng