Wani Bawan Allah Ya Mutu A Hanyarsa Ta Dawowa Daga Masallaci A Ranar Sallar Idi

Wani Bawan Allah Ya Mutu A Hanyarsa Ta Dawowa Daga Masallaci A Ranar Sallar Idi

  • Mutanen unguwan Okelele a Ilorin sun shiga zaman makoki bayan rasuwar wani bawan Allah sakamakon hatsarin mota a ranar Sallar Idi
  • Mutumin mai matsakaicin shekaru mai suna Suraju ya dako wasu mutane uku kan babur ne amma suka yi karo da wata mota a hanyarsu na dawowa daga masallaci
  • Rahotanni sun bayyana cewa Suraju ya ce ga garinku bayan an kai shi asibiti yayin da sauran wadanda suka jikkata suna asibiti ana musu magani

Jihar Kwara - Abin bakin ciki ya faru a Ilorin, Jihar Kwara, a ranar Juma'a, a lokacin da wani mutum mai matsakaicin shekaru ya rasa ransa sannan wasu uku suka jikkata sakamakon hatsarin mota.

Hatsarin da aka rahoto ya ritsa da mutane hudu ne da suke kan babur ne a hanyarsu na dawowa daga Sallar Idi a ranar Juma'a a Ilorin, The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Wani gini ya ruguje a barikin 'yan sanda, ya kashe, ya danne mutane da yawa

Taswirar Jihar Kwara
Wani Bawan Allah Da Ke Dawowa Daga Sallar Idi Ya Rasu A Haɗarin Mota A Jihar Kwara. Hoto: Nigerian Tribune
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran mutane ukun da ke kan babur din, wacce ta yi karo da motar, sun samu munanan rauni.

New Telegraph ta rahoto cewa an ce wadanda abin ya faru da su suna dawowa ne daga filin Idi na Ilorin lokacin da hatsarin ya faru a kusa da Balogun Fulani, a karamar hukumar Ilorin ta Kudu.

Marigayin, wanda aka ce sunsa Suraju, dan gidan Alamo ne daga Okelele a Ilorin.

City Round ta tatttaro cewa Suraju ya yi numfashinsa na karshe a wani asibiti da aka garzaya da shi don masa magani.

An birne shi a makabartar musulmi da ke Osere a Ilorin.

Mutane biyu cikin wadanda suka ji rauni an kwantar da su a Babban Asibitin Surulere, Ilorin, yayin da shi na ukun an kai shi wurin mai daurin karaya na gargajiya a unguwar Dada don masa magani.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Yi Alkawarin Cigaba da Kashe-Kashe Cikin Watan Azumi a Zamfara

Mutane da dama sun garzaya gidan su marigayin don yin ta'aziyya ga iyalansa.

Martanin Hukumar FRSC

Sakta Kwamanda na Hukumar Kiyayye Hadurra na Kasa, FRSC, na Jihar Kwara, Frederick Ogidan, ya ce ba a kawo rahoton afkuwar lamarin a ofishinsa ba.

Ya ce:

"Zan bincika in ji idan wani abu mai kama da haka ya faru, zan sanar da ku."

Bai riga ya kira majiyar Legit.ng ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Mutane 25 Sun Rasu, Wasu 10 Sun Jikkara A Hatsarin Mota A Bauchi

A wani rahoton kun ji cewa rayuka 25 sun salwanta sannan wasu mutane 10 sun jikkata a hatsarin mota a Bauchi.

Hadarin ya faru ne a hanyar Hadeja zuwa Potiskum da ke karamar hukumar Gamawa na Jihar Bauchi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164