Abun Bakin Ciki: Gobara Ta Lakume Shaguna a Kasuwar Kwara

Abun Bakin Ciki: Gobara Ta Lakume Shaguna a Kasuwar Kwara

  • Wata shahararriyar kasuwa ta Oja-Tuntun da ke yankin Baboko a Ilorin, jihar Kwara ta kama da wuta a daren Alhamis
  • Bayanai sun nuna cewa gobarar ta fara tasowa daga wani shago sannan ta yadu har zuwa wasu shaguna guda shida
  • Hukumar kwana-kwana ta daura alhakin tashin gobarar kan sakacin daya daga cikin masu shagunan

Kwara - Gobara ta tashi a shahararriyar kasuwar nan ta Oja-Tuntun da ke yankin Baboko da ke Ilorin, babban birnin jihar Kwara, Channels TV ta rahoto.

Annobar wacce ta fara tun a daren ranar Alhamis, 20 ga watan Afrilu, ta lalata shaguda shida daga cikin 1,070 da ke kasuwar.

Taswirar jihar Kwara
Abun Bakin Ciki: Gobara Ta Lakume Shaguna a Kasuwar Kwara Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Jaridar The Nation ta tattaro cewa an yi asarar kayayyaki na miliyoyin naira.'

Sakacin wani mai shago ne ya haddasa gobarar, hukumar kwana-kwana

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: An Kama Wasu Muggan Mutane Sama da 20 Ɗauke da Makamai Ana Dab da Sallah a Arewa

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle ya tabbatar da tashin gobarar, yana mai cewa jami'an hukumar sun shiga aiki don kashe wutan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Adekunle ya bayyana cewa shaguna shida abun ya shafa cikin shaguna 1,070 da ke kasuwar.

Ya kuma daura alhakin tashin gobarar a kan sakacin daya daga cikin masu shagunan.

A halin da ake ciki, daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Prince Falade John Olumuyiwa, ya taya Musulmai da yan Najeriya na gida da waje murnar bikin karamar sallah.

Ya shawarci mutane da su zamo masu lura yayin bikin "musamman da kayan girki yayin shirya abincinsu.

Yan bindiga sun kai hari kasuwar Ogun, sun kashe mutum daya

A wani labari na daban, mun ji cewa wasu tsagerun yan bindiga da ake zaton masu fashi da makami ne sunkai kazamin hari shahararriyar kasuwar wayoyi da kayan wuta da aka fi sani da 'Computer Village' a Abeokuta, jihar Ogun inda suka kashe wani dan kasuwa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Babbar Tashar Watsa Labarai a Najeriya Ta Kama Da Wuta a Watan Azumi

Yan bindigar da yawansu ya kai kimanin su takwas sun farmaki kasuwar da ke Oke-Ilewo, Abeokuta, da tsakar ranar Laraba, 12 ga watan Afrilu don aiwatar da aika-aikarsu.

Wasu da abun ya faru a kan idanunsu sun bayyana cewa maharan na ta harbe-harbe, lamarin da ya haddasa tashin hankali tsakanin yan kasuwa inda suka tsere don neman mafika.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng