"Sai Kace Zan Samu Tikitin Aljannah": Bidiyon Hijabin N1.8m Ya Janyo Cece-Kuce

"Sai Kace Zan Samu Tikitin Aljannah": Bidiyon Hijabin N1.8m Ya Janyo Cece-Kuce

  • Bidiyon wani hijabi da aka sanya masa farashin N1.8m ($4,500) ya yaɗu sosai a soshiyal midiya
  • Kuɗin da aka danƙarawa hijabin ya sanya masu amfani da yanar gizo yin kalamai na barkwanci sosai akan bidiyon, inda wasu ke tambayar ko harsashi baya huda shi
  • Mutane da dama sun bayyana ra'ayoyi mabanbanta akan kuɗin hijabin, inda da dama suka ce ya yi tsada sosai

Bidiyon wani hijabi wanda mata suke sanyawa da aka masa farashina N1.8m ($4,500), ya janyo cece-kuce a soshiyal midiya.

Bidiyon wanda ya janyo mutane suka yi ta maganganun barkwanci a kansa da cacccakar tsadar da hijabin ya yi, ya nuna hijabin luntsume da ƙwalliya mai ƙayatarwa.

Wani hijabi mai tsada ya janyo cece-kuce
Hotunan hijabin N1.8m Hoto: @7sisters_veils
Asali: TikTok

Wani shafin da ake sayar da kaya ne mai suna @7sisters_veils ya sanya bidiyon a manhajar Instagram.

Shafin ya yi ƙorafin cewa mutane sun dame su da ƙorafi akan kuɗin hijabin.

Kara karanta wannan

Hukuncin Addinin Musulunci Idan Bikin Idi Ya Hadu da Sallar Juma'a a Rana Daya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An bayyana mabanbantan ra'ayoyi kan farashin hijabin

Mutane da dama dai sun yi maganganu mabanbanta akan kuɗin da aka tsuga wa hijabin, inda suke cewa lallai ba za su iya cire kuɗin su ba su siya.

Ga kaɗan daga ciki:

theonlychioma ta rubuta:

"Ku dubi fa irin kwalliyar da akai masa. Ba zan yi mamaki ba idan da hannu ma aka ɗinka shi."

zaynab_azeez ta rubuta:

"Ba wai maganar kuɗin ba amma shin hijabin ya yi kama da kuɗin da aka sanya masa? Gwara na je na ɗinka rigar amarci na sanya mutum uku su riƙe min ita a baya mu tafi Eid…saafu iwaju."

ejemarray ya rubuta:

"Ya yi tsada sosai ne kawai saboda an sauya kuɗin zuwa naira. Ban da tabbacin cewa yayi tsadar hakan a ainihin kuɗin da akai masa farashi."

_zelda01 ta rubuta:

Kara karanta wannan

Abun Kallo: Wata Amarya Ta Fusata Ta Hukunta Mijinta Kan Laifi 1, Bidiyon Ya Girgiza Mutane

"Shin zai bani tikitin shiga Aljannah kai tsaye ne?

asiyah_dalhat ta rubuta:

"Babu wani abu na musamman akan wannan hijabin. Ehen na faɗa na ƙara faɗa."

Magidanci Ya Yi Wa Mai Koyon Aiki Wajen Matarsa Ciki

Mun kawo mu ku rahoto kan yadda wani magidanci ya bi son zuciya ya yi wa mai koyon aiki wajen matarsa ciki.

Magidancin ya ce ai ta san hannun ta akan gado, hakan ya sanya ya maƙale mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng