Rikicin Sudan: Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilin Da Ya Sanya Ta Kasa Kwaso 'Yan Najeriya
- Gwamnatin tarayya tace tana iyakar bakin ƙoƙarin ta wajen ganin ta kwaso ƴan Najeriya da rikicin Sudan ya ritsa da su a ƙasar
- Gwamnatin tace ta buƙaci hukumomin ƙasar da su yarje mata ta fara jigilar ƴan Najeriyan da suka maƙale a can
- Rashin mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da ɓangarorin biyu masu faɗa da juna suka yi shine ya ke bayar da matsala wajen kwaso mutanen
Abuja - Gwamnatin tarayya ta roƙi hukumomi a ƙasar Sudan da su bayat da izinin ta kwaso ƴan Najeriya da ke ƙasar, yayin da ake ci gaba da fafata rikici a ƙasar.
Gwamnatin tarayyar ta bayyana cewa rashin mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma, shine ya sanya ba zai taɓa yiwuwa ta faro kwaso ƴan Najeriyar da rikicin ya ritsa da su a ƙasar ba, rahoton The Cable ya tabbatar.
Shugaba Buhari Ya Aike Da Sakon Murnar Sallah Ga 'Yan Najeriya, Ya Bayyana Wata Babbar Nasara Da Ya Samu
Kakakin ministirin harkokin ƙasashen waje, Francisca Omayuli, ta bayyana a ranar Alhamis cewa ƙasar nan ta damu matuƙa kan yadda wutar rikicin ke ƙara ruruwa.
A kalamanta:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ƙin sauraron da ɓangarorin biyu masu faɗa da juna suka yi na kiraye-kirayen tsagaita wuta da ƙashen duniya suka yi, ya ƙara sanya mutane cikin halin tasku sannan ya sanya ba zai taɓa yiwuwa a kwaso su ba. A dalilin haka Najeriya tana kiran da a tsagaita wuta cikin gaggawa."
"A halin da ake ciki ministirin mu na tuntuɓar hukumomin ƙasar Sudan ta hannun ofishin jakandacin Najeryiya da ke Khartoum domin neman izinin kwaso ɗalibai ƴan Najeriya da sauran ƴan Najeriyan da suke son su baro ƙasar."
Ministirin ta kuma ƙara da cewa ta ƙirƙiri dandali a WhatsApp da Telegram domin samar da cikakkun bayanai da ƙarin haske, cewar rahoton Headtopics
An kuma shawarci ƴan Najeriyan da rikicin ya ritsa da su a ƙasar da su ci gaba da zama cikin gidajen su.
Shugaba Buhari Ya Nemi A Tsagaita Wuta a Sudan
A wani rahoton na daban kuma, shugaba Buhari ya sanya baki akan rikicin da ga ɓrke a ƙasar Sudan. Shugaban ƙasar ya nemi ɓangarorin biyu da su kai zuciya nesa.
Faɗa dai ya ɓarke a ƙasar ta Sudan tsakanin sojoji masu biyayya ga gwamnati da kuma dakarun da ke biyayya ga wani babban Janar na soja da ke ƙoƙarin karɓe mulki a ƙasar.
Asali: Legit.ng