Gwamnan Jihar Benue Ya Dau Zafi, Ya Yi Wa Shugaba Buhari Kakkausan Martani

Gwamnan Jihar Benue Ya Dau Zafi, Ya Yi Wa Shugaba Buhari Kakkausan Martani

  • Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya mayar da martani mai zafi kan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari
  • Gwamna Ortom ya ce shugaban ƙasar bai damu ba ko.kaɗan wajen kare rayukan al'ummar ƙasar nan
  • Ortom na mayar da martani ne bayan gwamnatin Buhari ta ɗora laifin kashe-kashen da ke aukuwa a jihar a kansa

Jihar Benue - Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya caccaki shugaba Buhari bisa ɗora laifin kashe-kashen da ake fama da su a jihar akan gwamnatin sa.

A ranar fadar shugaban ƙasa tace gwamna Ortom ne ke da laifi kan kashe-kashen da ke aukuwa a jihar, inda ta yi zargin cewa gwamnan ya yi fatali da ƙoƙarin da shugaba Buhari ya yi na shawo kan matsalar.

Ortom ya caccaki shugaba Buhari
Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom Hoto: Leadership.com
Asali: UGC

Da ya ke mayar da martani a ranar Alhamis, gwamna Ortom ya bayyana kalaman na fadar shugaban ƙasa a matsayin ƙoƙarin sauya yadda haƙiƙanin abubuwa suke, rahoton The Cable ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Ana Dab Da Rantsar Da Tinubu, Nasir El-Rufa'i Ya Hango Wata Babbar Matsala Mai Barazana Ga Mika Masa Mulki

A wata sanarwa da Nathaniel Ikyur, kakakin gwamnan jihar ya fitar, gwamna Ortom ya ce shugaba Buhari ya gaza wajen kare rayukan mutanen ƙasar nan, musamman mutanen jihar Benue.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Shugaban ƙasa ya nuna cewa a sanarwar nan da ya fitar ta kwanan nan, ya fi fifita shanu akan rayukan al'umma wanda hakan cin fuska ne ga mutanen da aka halaka a jihar Benue da sauran sassan ƙasar nan. Idan ba haka ba me yasa zai yi wa mutanen da ke kwance a kabarin su shagube."
"Wannan cin mutunci ne ga mutanen Benue ciki har da waɗanda aka halaka, ƙananan yaran da aka yanka kamar kaji, matan da aka keta haddin su da sama da mutum miliyan 2 da suke rayuwa a sansanin ƴan gudun hijira ma fi girma a jihar nan"

Gwamna Ortom ya bayyana cewa mummunan kisan kiyashin da ake a jihar sa, wani shiri ne da Fulani suka shirya akan mutanen jihar domin ƙwace mu su gonakin su na gado, cewar rahoton Punch

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Shugaba Buhari Ya Tona Asirin Wani Gwamnan Arewa Wanda Ya Sha Kaye a Zaɓen 2023

Tinubu Ya Kafa Kwamitin Rantsar Da Shugaban Kasa

A wani rahoton na daban kuma, kun ji yadda zaɓaɓɓen shugaban ƙasa ya kafa kwamitin kula da rantsar da shugaban ƙasa.

Kwamitin yana ƙunshe ne da sunan wasu manyan ƴan Najeriya mutum 13, waɗanda za su kula da rantsar da Bola Tinubu a matsayin sabon shugaban Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng