“Kin Yi Hikima”: Martanin Jama’a Bayan da Mata Ta Gano Mijinta Zai Kara Aure, Ta Yashe Kudadensu

“Kin Yi Hikima”: Martanin Jama’a Bayan da Mata Ta Gano Mijinta Zai Kara Aure, Ta Yashe Kudadensu

  • Wata mata ‘yar Najeriya da ta gano mijinta na son kara aure ta yi maganinsa, ta san yadda ta yi da kudinta
  • Matar ta gaggauta cire dukkan kudin da ke cikin asusunsu na hadin gwiwa yayin da ta gani ya kashe kusan 50%
  • Mutane da yawa a kafar sada zumunta sun yi mamaki, sun ce matar ta yi dabara, kuma ta san hanyar neman mafita

Wani matashin dan Najeriya, @prince_dstn ya yada wani bidiyo da ke nuna yadda ya yi kokarin shiga tsakanin a rikicin da ya kunno kai tsakanin miji da mata.

A cewarsa, mutumin ya kawo karar matarsa ne sabida ta kashe dukkan kudin da ke cikin asusunsu na hadin gwiwa ba tare da sanar da shi ba.

Da yake magana da ma’auratan, matar tana da kudi N700k a matsayin gadonta, inda mijin ya shawarce ta da su sayi filin don ginawa.

Kara karanta wannan

Abun Kallo: Wata Amarya Ta Fusata Ta Hukunta Mijinta Kan Laifi 1, Bidiyon Ya Girgiza Mutane

Rikici tsakanin miji da mata
Mata da miji na rikici | Hoto: @prince_dstn
Asali: TikTok

Bayan wani dan lokaci, mijin ya siyar da filin tare da cin riba sai kawai ya fara kokarin kara aure ba tare da ya sanar da ita ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya siyar da filin akan N1.5m, yayin da matar ta ji labarin abin da yake son yi da kudin, nan take ta cire N800k daga asusun kasancewar mijin ya riga ya kashe wani adadi na kudin.

Mijin ya yi kokarin yadda zai kare kansa, amma haka dai suka gaza samun matsaya saboda kowa na da hujjarsa.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a

baby girl:

"Macen Hakimi, shawari mai kyau.”

user8241571664427:

"Wannan mata bari na tambaye ki, a ina kika hadu da wannan wawan namijin kika aura? Na gaji da wasu matan wallahi.”

user5254669997717:

"N700K a hada 100k a matsayin riba magana ta kare.”

Kara karanta wannan

Bayan Shafe Shekaru a Amurka, Matashiya Ta Dawo Najeriya Ta Ga Lalataccen Gidan Da Dan Uwanta Ya Gina Mata, Ta Sharbi Kuka

Rita Wuese:

"Mu ‘yan kungiyar mata Hakimi muna alfahari da ke.”

Chinka Ogbonna:

"A zahirance dukan 1.5m na matar ne. Magana ta gaskiya mutumin ya kashe rabonsa, wancan 800 na rabon matar ne a dokance.”

vivimaasie:

"Kungiyar mata ‘yan uwan juna na alfahari da ke.”

Nigeria boy:

"Wannan mutumin bai da hankali ko kadan, ina jinjina ga matar bisa wannan wayon na hana kawo mata ta biyu, na ji kamar na taya ka kuka malam.”

Wata mata kuwa cewa ta yi, ba za ta iya auren mutumin da kudin shigansa bai haura N70k ba saboda wasu dalilai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.