Cece-Kuce Ya Kare, Mahaifiyar Hakimi Ta Ce Bata San da Danta Ya Sanya Sunanta a Kadarorinsa Ba

Cece-Kuce Ya Kare, Mahaifiyar Hakimi Ta Ce Bata San da Danta Ya Sanya Sunanta a Kadarorinsa Ba

  • Mahaifiyar dan wasan kwallon kafa Hakimi ta yi bayani game da tushen dukiyarsa da inda yake kaita
  • A cewar mahaifiyar tasa, bata san da labarin cewa danta ya kasa dukiyarsa zuwa asusun bankinta ba
  • An yada jita-jita game da yadda Hakimi ya rabu da matarsa da kuma yadda rikici ya barke kan rashin kudinsa

Kasar Maroko - Mahaifiyar dan wasan kwallon kafan Maroko da PSG Achraf Hakimi, Saida Mouh ta yi martani game da jita-jitan cewa danta ta maka sunanta kan dukkan kadarorinsa.

A cewar Saida, bata san da hakan ba, kuma bata shirya hakan tare dan nata ba, rahoton jaridar Vanguard.

A makon da ya gabata, kafar sada zumunta ta rikice bisa jin labarin rabuwar Hakimi da matarsa Hiba Abouk, inda aka ce ba za ta samu rabin dukiyarsa ba kamar yadda dokar turawa ta tanada.

Kara karanta wannan

Bayan Shafe Shekaru a Amurka, Matashiya Ta Dawo Najeriya Ta Ga Lalataccen Gidan Da Dan Uwanta Ya Gina Mata, Ta Sharbi Kuka

Hakimi: Mahaifiyar dan kwallo ta yi bayani
Hakimi da matarsa da kuma mahaifiyarsa | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Abin da kuma yasa hakan ya faru, ance Hakimi ya yi hikimar kakaba sunan mahaifinsa ne kan duk wani abu da ya mallaka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bansan komai ba, inji mahaifiyar Hakimi

A ranar Laraba, mahaifiyar Hakimi ta yi bayani a lokacin da take tattaunawa da kafar labaran Maroko na Morocco World News, inda tace danta bai sanar da ita komai game da tura mata dukiyarsa ba.

A cewarta:

“Idan ya dauki wani matakin kare kansa, to ni dai ban sani ba. Meye matsala idan ma labarin gaskiya ne? Idan da na bai yi haka ba ba zai samu damar rabuwa da waccar matar ba [Hiba Abouk].”

Bayanan mahaifiyar Hakimi na nuni da alamar cewa, akwai ‘yar tsama a tsakaninsu, kuma tuni suka rabu a watan jiya.

Hiba ba za ta samu anini daga dukiyar Hakimi ba

Kara karanta wannan

Karin bayani: Bayan kammala zabe, an sace direban mataimakin gwaman Arewa

A cewar rahotanni, Hiba ba za ta samu ko anini ba daga dukiyar Hakimi duk da kuma sun raba igiyar aurensu saboda babu ko kadara daya da ke like da sunansa.

Kafar labaran Sifaniya, Marca ta ruwaito a ranar Juma’a cewa, Hiba ta nemi kotu ta kwaci rabin dukiyar Hakimi, amma aka gano fakiri ne bai da anini da sunansa.

A cewar jaridar, dukkan albashi da kudaden shigan Hakimi na gangarawa ne zuwa asusun mahaifiyarsa.

Hakimi dai na daya daga cikin ‘yan wasan da ke shan romon kwallon kafa, inda yake kwasar miliyoyi a duk mako.

Tuni dai maza suka fara daukar salo irin na Hakimi, suke ganin abin da ya aikata daidai ne kuma yi maganin mata 'lashe-moni'.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.