Gwamnatin Tarayya Ta Yi Wa Shugaban Wata Babbar Hukuma Ritayar Dole, Ta Bayar Da Dalilai
- Gwamnatin tarayya ta umarci shugaban hukumar kula da shige da fice ta ƙasa da ya yi ritaya
- Gwamnatin ta ɗauki wannan matakin ne biyo bayan ƙaratowar wa'adin ƙarshen wa'adin mulkin sa
- An umarci shugaban, Isah Jere, da ya miƙa ragamar shugabancin hukumar ga babban jami'in hukumar da ke bi masa
Abuja - Gwamnatin tarayya ta umarci Kwantirola Janar na hukumar shige da fice ta ƙasar nan (NIS), Isah Jere, yayi ritaya.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa sanarwar hakan na ƙunshe ne a wata takarda hukumar kula da harkokin Civil Defence, Correctional, Fire da Immigration, ta fitar ranar 17 ga watan Afirilun 2023, ta aikewa shugaban hukumar NIS.
A takardar an umurci shugaban hukumar da ya miƙa ragamar gudanarwar hukumar ga babban jami'i a hukumar.
Jaridar Punch tace umarnin na zuwa ne biyo bayan zargin da ake yi cewa shugaban hukumar ta NIS yana ƙoƙarin ganin an ƙara masa wa'adin mulkin sa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Isah Jere a watan Afirilun shekarar da ta gabata ne a ka ƙara masa wa'adin shekara 1 kafin ya yi ritaya.
Wasu daga cikin jami'an hukumar sun yi barazanar yin zanga-zanga idan gwamnatin tarayya ta ƙara tsawaita wa'adin sa a karo na biyu.
Wani bangare na takardar na cewa:
"Na rubuto wannan takardar domin janyo hankalin ka kan ƙarshen ƙarin wa'adin shekara 1 da shugaban ƙasa ya yi maka a cikin takarda mai lamba SH/COS/42/3/3/A128 ta ranar 22, ga watan Afirilun 2022, wanda wa'adin zai ƙare a ranar 24 ga watan Afirilun 2023."
"A dalilin hakan ana umartar ka da ka miƙa ragamar shugabancin hukumar ga babban mataimakin Kwantirola Janar na hukumar a ranar ko kafin ranar Litinin, 24 ga watan Afirilun 2023, kafin zuwan lokacin da shugaban ƙasa zai naɗa sabon shugaban hukumar."
Idris Jere ya kama aiki a matsayin shugaban riƙo na hukumar kula da shige da fice ta ƙasa, a watan Satumban 2021, bayan tsohon shugaban hukumar Muhammad Babandede, ya yi ritaya.
Mummunan Hadarin Mota Ya Janyo Asarar Rai
A wani rahoton na daban kuma, kun ji yadda wani mummunan haɗarin mota ya janyo asarar rai, ya yin da wasu mutane da dama suka jikkata a jihar Legas.
Haɗarin dai ya auku ne bayan wasu motocin haya guda biyu sun yi taho mu gama da juna.
Asali: Legit.ng