Zan Yi Tattaki Daga Jihar Benue Har Abuja Saboda Tinubu, Inji Wani Matashi Jigon APC

Zan Yi Tattaki Daga Jihar Benue Har Abuja Saboda Tinubu, Inji Wani Matashi Jigon APC

  • An samu wani matashi kuma shugaban tawagar gangamin APC da yace zai yi tattaki daga Benue zuwa Abuja a kafa
  • Ya ce zai shaida ganin yadda za a rantsar da Bola Ahmad Tinubu a watan Mayu, don haka yake kira a taya shi tattakin
  • Ba wannan ne karon farko da ‘yan Najeriya ke wanke kafa don yin tattaki saboda ganawa da shugaban kasa ba, an yi hakan da dama

Jihar Benue - Shugaban kungiyar goyon bayan Tinubu ta Benue Youth Volunteers for Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Kwamared David Aper Nyor ya bayyana aniyarsa ta yin tattaki a kafa daga Makurdi zuwa Abuja don shaida rantsar da sabon shugaban kasa.

Nyor, wanda dan asalin karamar hukumar Konshisha ne ya ce, zai yi wannan tattaki ne domin nuna farin cikinsa da zaben Bola Ahmad Tinubu na APC, Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tausayi Ko Tsautsayi: Daga Kan Buhari, Jerin Yan Takarar Da Suka Sharbi Kuka Kan Talaka a Tv

Idan baku manta ba, Bola Ahmad Tinubu ne ya lashe zaben shugaban kasan Najeriya da aka gudanar a watan Faburairun bana.

Matashi zai yi tattakin ganin Tinubu daga Benue zuwa Abuja
Bola Ahmad Tinubu zababben shugaban Najeriya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Za a rantsar da Tinubu, babu mai hanawa

A bayanin da Nyor ya yi, ya ce tattakin nasa zai zama sharar fage da kuma akwar da shakkan magauta da ke ganin ba za a rantsar da Tinubu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma kara da cewa, duk wani mai tunanin cewa Tinubu ba zai ciyar da kasa gaba ba to makiyin Najeriya na gaske wanda bai son zaman lafiya da hadin kai.

A jawabinsa:

“Da kaina zai halarci taron rantsar da zababben shugaban kasa ta, a matsayin mai aikin sa kai. Zan yi tattaki daga ofishin kamfen Tinubu/Shettima da ke Makurdi zuwa Abuja daga ranar rantsarwa don karrama nasarar Asiwaju.”

Ku zo mu yi tattaki tare, Nyor ga ‘yan Najeriya masu kishin kasa

Kara karanta wannan

An saka maku ciwon kai: Bayan turmushe Binani, Fintiri ya yiwa 'yan jihar Adamawa jawabi

Ya yi kira ga ‘yan kasa masu kishi da su taso tare da yin wannan tattaki tare dashi don tallata gwamnati ta gari da kuma samar da gobe mai kyau ga Najeriya, Idoma Voice ta tattaro.

A cewar Nyor, ‘yan Najeriya sun zabi Tinubu ne saboda sun yarda dashi da kwazonsa har da gogewarsa wajen ceto kasar.

Tafiyar Nyor dai ba komai bace a cewarsa face nuna jajircewa da mubaya’a ga sabon shugaban kasan Najeriya Tinubu da jam’iyyar APC.

A baya dama wani gwamna ya ce babu wanda ya isa duk duniyar nan ya hana rantsar da Bola Ahmad Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.