“Yana Ta Kashe Kudi Son Ransa”: An Turawa Mai POS Miliyan N280 Bisa Kuskure, Ya Kashe Su

“Yana Ta Kashe Kudi Son Ransa”: An Turawa Mai POS Miliyan N280 Bisa Kuskure, Ya Kashe Su

  • Wani mai POS ya samu alat din naira miliyan 280 da aka tura asusun bankinsa bisa kuskure
  • Ba tare da tunanin komai ba, ya bazama kashe kudaden har sai da aka bankado inda yake tare da kwamushe shi
  • Makwabta sun damu da ganin cewa mutumin da ke samun yan dubbai kadan zai iya kashe makudan kudade haka harda siyan motoci

Kwara - An kama wani mai POS da aka bayyana da suna Alfa Rafiu a jihar Kwara kan zargin kashe naira miliyan 280 da aka tura asusunsa bisa kuskure, Nigerian Tribune ta rahoto.

An tattaro cewa wanda ake zargin mazaunin Akuji da ke yankin Abayawo a karamar hukumar Ilorin ta yammacin jihar.

Jami'an yan sanda da bindigogi
“Yana Ta Kashe Kudi Son Ransa”: An Turawa Mai POS Miliyan N280 Bisa Kuskure, Ya Kashe Su Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Yadda miliyoyi suka shiga asusun bankin mai POS

A cewar majiyoyi da ke da masaniya kan lamarin, kwatsam aka ga Rafiu yana ta kashe-kashen kudi bayan ya samu shigar miliyoyin naira cikin asusunsa yan makonni da suka gabata.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Za Tayi Wa Ma’aikata Karin Albashi a Afrilu Saboda Cire Tallafin Fetur

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Kimanin makonni biyu da suka gabata, ya samu alat da ya kai miliyan 280 wanda bai da masaniyar komai a kansa.
“Sai dai maimakon ya ja hankalin bankin da ya tura masa wannan makudan kudin bisa kuskure, sai ya hau kashe su cikin sauri.
“Rafiu ya siya gidaje, motoci sannan ya tura mutane Umrah. Wasu daga cikin wadanda ya dauki nauyinsu suna Saudiyya a yanzu haka da muke magana.
“Koda dai ya yi wa mutane da dama alkhairi a garin, wasu mazauna sun yi mamaki gane da yadda ya yi kudi farat daya a matsayinsa na mai POS.”

An tattaro cewa yan sanda daga ofishin “C” Division da ke Oja-Oba, Ilorin sun kama wanda ake zargin da rakiyar wasu jami’an banki.

Da jaridar Daily Trust ta ziyarci yankin nasa a ranar Talata, shagon POS dinsa ya kasance a rufe sannan wasu mazauna gidan sun ce ya yi tafiya basu san yaushe zai dawo ba.

Kara karanta wannan

Kaico: Bashi ya yi mata katutu, ta siyar da jaririyarta mai watanni 18 kacal a wata jiha

Da aka tuntube shi, Kakakin yan sandan jihar Kwara, Ajayi Okasanki ya tabbatar da lamarin.

“Eh, da gaske ne, amma sashin FCIID daga Alagbon-Close, Ikoyi, Lagas ne suka aiwatar da kamun nasa wanda hakan ya fita daga hannunmu."

Ba zan iya auren matar da ke karbar N5m albashi ba duk wata, matashi

A wani labari na daban, wani matashi ya baiwa mutane da dama mamaki a soshiyal midiya bayan ya ce shi ba zai iya auren macen da ke karbar naira miliyan 5 duk wata a matsayin albashi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng