Biyo Bayan Katobarar Da Yayi a Adamawa, Sanannen Malamin Addinin Musulunci Ya Caccaki Hudu Ari
- Wani sanannen malamin addinin musulunci a jihar Bauchi, ya yi wa Hudu Yunusa Ari wankin babban bargo
- Dr Idris Abdulaziz ya bayyana cewa abinda Hudu ya yi a jihar Adamawa ya zubar da ƙimar mutanen jihar Bauchi
- Malamin addinin ya ce har shawara da nasiha ya yiwa Hudu amma ya sanya ƙafa ya yi fatali da su
Jihar Bauchi - Malamin addinin musulunci a jihar Bauchi, Dr Idris Abdulaziz, ya bayyana dakataccen kwamishinan zaɓen INEC na jihar Adamawa, Hudu Yunusa Ari, a matsayin abin kunya ga jihar Bauchi.
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa malamin addinin ya kira Hudu da hakan ne bisa bayyana Aisha Dahiru Binani, ta jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wacce ta lashe zaɓen zaɓen gwamnan jihar Adamawa.
Wannan katoɓara da kwamishinan zaɓen yayi, ya sanya hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta buƙaci sufeto janar na ƴan sanda, da ya tuhume sa, cewar Rahoton The Cable.
A wani faifan bidiyo da ya karaɗe soshiyal midiya, malamin ya bayyana cewa abinda kwamishinan ya yi ya ɓata masa rai matuƙa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dr Abdulaziz ya kuma bayyana cewa kwamishinan ya zubar wa da mutanen jihar ƙima a idon duniya.
A kalamansa:
"Na yi baƙin ciki da jin haushin abinda wani ɗan jihar mu, Hudu Yunusa, ya yi. Ya kunya ta mutanen jihar Bauchi da kuma na ƙaramar hukumar sa ta Ningi."
"Hudu, ka zubar mana da ƙima. Hakan ya nuna baka san abinda kake yi ba kuma ka ƙi ɗaukar jan kunnen da na yi maka."
"Lokacin da aka gabatar da shi a matsayin wanda za a ba kwamishina, ya tuntuɓe ni inda na gaya masa cewa ba zan taya shi murna ba, amma zan yi masa nasiha ya ji tsoron Allah sannan yayi gaskiya."
"Lokacin da na samu labarin an tura shi Adamawa, sannan an bayyana zaɓen matsayin wanda bai kammalu ba, na yi masa nasiha inda na tura masa saƙon waya, wanda ya yi martanin cewa ya gode sosai."
Dr. Abdulaziz sananne ne wajen yin wa'azin kada a zaɓi mata a kujerun mulki na siyasa.
Ba da Mace Nayi Takara ba – Fintiri ya Fadi Asalin Abokan Gwabzawarsa
A wani labarin na daban kuma, gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya bayyana da haƙiƙanin waɗanda yayi takara da su a zaɓen gwamnan jihar.
Fintiri ya ce ba da Binani ya yi takara da wasu ne waɗanda ba sa son cigaban dimokuraɗiyya a Najeriya.
Asali: Legit.ng