“Soyayya Ruwan Zuma Dadi”: Tsohuwa Rike Da Sanda Ta Amarce Da Sahibinta a Bidiyo

“Soyayya Ruwan Zuma Dadi”: Tsohuwa Rike Da Sanda Ta Amarce Da Sahibinta a Bidiyo

  • Wani bidiyon TikTok ya nuna lokacin da wata tsohuwar mata ta shiga daga ciki tare da sahibinta
  • Bidiyon wanda ya samu mutun 176k da suka kalla ya nuna cewa matar ta bayyana filin biki da sandar dogarawarta
  • Jajircewarta na ganin ta auri sahibinta duk da tsufanta ya haddasa cece-kuce a tsakanin masu amfani da TikTok

Matasa a manhajar TikTok sun jinjinawa wata mata da ta amarce da sahibinta duk da yawan shekarunta a duniya.

A bidiyon wanda shafin @mbhdirector ya wallafa, matar ta bayyana a wajen shagalin bikinta da taimakon sandar da take dogarawa.

Tsohuwa da angonta sun shiga daga ciki
“Soyayya Ruwan Zuma Dadi”: Tsohuwa Rike Da Sanda Ta Amarce Da Sahibinta a Bidiyo Hoto: @mbhdirector.
Asali: TikTok

An gano wani mutumi da ake tunanin mijinta ne yana tafiya a gefenta a cikin wani gajeren bidiyo mai tsawon sakanni 30.

Bidiyon tsohuwa cikin rigar amare ya yadu a TikTok

Kara karanta wannan

“Ta Gaji Da Auren Tun Ba a Kai Koina ba” Bidiyon Amarya Tana Kicin-Kicin Da Rai Yayin da Take Jerawa Da Angonta Ya Yadu

Tana ta tafiya a hankali zuwa wajen binkinsu yayin da taron yan taya murna ke ta jinjina masu tare da yin wake-wake a coci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yanayi ne na farin cikin domin taron jama'ar sun kasa boye jin dadinsu lokacin da ma'auratan suka bayyana.

Mutane da dama sun bayyana auren tsohuwar a matsayin mafarki da ya zama gaskiya a gareta.

Ba a gane a ina ne aka dauki bidiyon ba, amma dai ya shahara kuma ta ja hankali sosai a TikTok.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@rebeccaasante20 ya ce:

"Allah ya karo albarka."

@AwuraAkua ya ce:

"Waooooooo, ina maku addu;an jarin shekaru masu albarka."

@Famatta Nagbe ta yi martani:

"Rayuwar aure mai albarka umma da Abba."

@ellaogochimere ya ce:

"Rayuwar aure mai albarka."

@God's Eye ta yi martani:

"Lokacin Allah."

@sylvia ta yi martani:

"Karshen ya fi farkon."

Kara karanta wannan

“Suna Rayuwa Kamar Tagwaye” Matashi Ya Yada Bidiyon Kyawawan Matansa 2 Sanye Da Kaya Iri Guda

@user269230499195 ya ce:

"Soyayya abu ne mai kyau."

Bidiyon wata amarya cikin yanayi na bakin ciki ya yadu, jama'a sun yi martani

A gefe guda, bidiyon shagalin bikin wasu ma'aurata ya bar baya da kura bayan an gano amaryar cikin wani irin yanayi mara kyawun gani.

Amaryar ta yi kicin-kicin da fuska yayin da suke jerawa da angon zuwa filin shagalin bikinsu lamarin da ya sa mutane tunanin ko dai auren dole aka yi mata ba na soyayya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng