Mummunan Rikici Ya Barke Tsakanin Makiyaya Da Manoma a Jihar Plateau

Mummunan Rikici Ya Barke Tsakanin Makiyaya Da Manoma a Jihar Plateau

  • Wani mummunan rikici da ya ɓarke a jihar Plateau ya lamushe rayukan gwamman mutane a jihar
  • Rikicin ya ɓarke ne a tsakanin makiyaya da manoma a cikin ƙaramar hukumar Mangi ta jihar
  • Baya ga asarar rayukan mutane da dama, an kuma ƙona gidaje masu tarin yawa mummunan rikicin

Jihar Plateau - Mutane da dama sun halaka sannan an ƙona gwamman gidaje a wani mummuna faɗa da ya ɓarke tsakanin makiyaya da manoma a ƙauyen Tumbi, cikin ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Plateau.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa rikicin ya fara ne ranar Juma'a, sannan har ya zuwa lokacin kammala haɗin wannan rahoton ana ci gaba da fafatawa tsakanin ɓangarorin biyu.

An halaka mutane da dama a rikicin jihar Plateau
Rikicin ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dama Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Wani mazaunin ƙauyen mai suna Ibrahim Musa ya bayyana cewa ɗaruruwan mutane sun tsere daga ƙauyen, sannan ya ce an ƙona gidaje sama da guda ɗari.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Sanya Baki a Rikicin Sudan, Ya Aike Da Wani Muhimman Sako

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Har yanzu ana cigaba da rikicin. Ɗaruruwan mutane na guduwa daga ƙauyen. Ba zan iya cewa ga haƙiƙanin mutanen da aka kashe ba, amma an kashe mutane da dama. An ƙona gidaje fiye da guda 100"

Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya bayyana cewa an tura dakarun sojojin Operation Safe Haven (OPSH) zuwa yankin domin dawo da doka da oda, cewar rahoton Mynigeria

"Bana son na bayar da adadin da ke cin karo da juna. An tura jami'an tsaro zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya." A cewarsa

An yi Allah wadai da rikicin

Darekta Janar na ƙungiyar samar ta zaman lafiya ta Plateau State Peace Building Agency (PPBA), Joseph Lengmang, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya bayyana cewa:

Kara karanta wannan

An Samu Asarar Rai Da Dukiyoyi Kan Mummunan Rikicin Sarauta a Wata Babbar Jihar Arewa

"Mun yi baƙin ciki sosai kan munanan abubuwan da ke faruwa a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Plateau, inda rahotanni suka nuna taɓarɓarewar tsaro a wasu yankunan ta wanda yayi sanadiyyar asarar rayukan mutanen da basu ji ba basu gani ba da lalata dukiyoyi."

An Samu Asarar Rai Da Dukiyoyi Kan Rikicin Sarauta a Wata Babbar Jihar

A wani rahoton kuma, kun ji yadda rikicin sarauta a jihar Bauchi ya janyo asarar rai da dukiyoyi masu tarin yawa a jihar Bauchi.

Rikicin dai ya ɓarke ne bayan wasu matasa masu adawa da naɗin da aka yiwa wani basarake sun fara afkawa kan mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng