Labari Mai Ban Takaici Na Yadda Wata Matar Aure Ta Siyar da Jaririyarta a Jihar Ogun

Labari Mai Ban Takaici Na Yadda Wata Matar Aure Ta Siyar da Jaririyarta a Jihar Ogun

  • An kama wata matar da ta siyar da diyarta a jihar Ogun saboda tsananin bashin da ta ci a wani bankin kasuwanci
  • Rahoto ya bayyana yadda matar ta shiga tashin hankali da kuma matsin da ya kai ta ga barin garinsu zuwa jihar Legas
  • Ba wannan ne karon farko da ake samun yanayi mai tada hankali kamar wannan ba, hakan ya sha faruwa a lokuta mabambanta

Jihar Ogun - ‘Yan sanda a jihar Ogun sun kame wata mata mai shekaru 33, Olaide Adekunle da laifin siyar da jaririyarta mai watanni 18 a kan kudi N600,000 don warware bashin da banki ke binta.

Wacce ra siya, da har yanzu ake nema ta sayi jaririyar ne a birnin Legas da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda, Abimbola Oyeyemi ne ya shaidawa manema labarai wannan mummunan labarin a birnin Abeokuta na jihar a ranar Litinin 17 Afirilu, 2023, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Innalillahi: An shiga tashin hankali, shugaban APC a wata jiha ya fadi matacce

Mata ta siyar da diyarta
Matar da ta siyar da diyarta a Ogun | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A cewarsa, an kame wacce ake zargin ne bayan da mijinta, Nureni Rasaq ya kai rahoto game da lamarin a hedkwatar ‘yan sabda da ke Sango.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda matar ta tafi Legas a watan Maris

Oyeyemi ya bayyana cewa, mijin ya ce matarsa ta yi tafiya zuwa Legas a watan Maris tare da ‘yarsu mai suna Moridiat Rasaq, amma ta dawo hannu rabbana ba tare da jaririyar ba.

Ya kara da cewa, mijin ya ce ya yi kokarin jin meye ya faru, amma abin ya ci tura, kuma ya gaza gane inda jaririyar tasu take.

Daga nan ne DPO na Sango, Dahiru Saleh ya hada jami’ai tare da tabbatar da kwamushe matar da ake zargi da mummunan aiki, kafar Tori ta tattaro.

Oyeyemi yace, bayan gudanar da bincike, matar ta amsa cewa ta siyar da diyar tata a kan kudi N600,000.

Kara karanta wannan

“Biza Dole”: Dattijuwar Mata Ta Shigo Najeriya Daga Amurka, Ta Yi Wuff Da Hadadden Saurayi a Bidiyo

Dalilin da yasa ta siyar da jaririyar

Da aka tambaye ta dalilin yin hakan ta ce, ta ci bashin wani banki ne, amma ta gaza biya, don haka suka yi ta mata barazana, wanda saboda haka ta koma Legas domin tallan ruwan leda.

A cewar jami’in dan sandan:

“A lokacin da take tallan ne ta hadu da mutumin da ya gabatar da ita ga wata mata da daga baya ta siya jaririyar a Legas.”

Ya kara da cewa, mukaddashin kwamishinan ‘yan sandan jihar, DCP Babakura Muhammad ya umarci a mayar da lamarin gaban cibiyar binciken manyan laifuka don tsananta bincike.

A baya, wata mata ta siyar da diyar ta saboda tsananin talaucin da ya sanya ta cikin halin kakani-kayi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.