Talauci da tsananin rayuwa ce ta sa na sayar da jinjira ta - Mata mai shekaru 20

Talauci da tsananin rayuwa ce ta sa na sayar da jinjira ta - Mata mai shekaru 20

- Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta damke wata mata mai shekaru 20 da laifin siyar da diyarta

- Kamar yadda rundunar ta bayyana, ta siyar wa wasu mutum biyu jinjirar a kan N130,000 amma ta ce talauci ne ya saka ta gaba

- Wasu ma'auratan da suka kwashe shekaru 15 babu haihuwa ne suka siya jinjirar a kan N150,000 daga hannun 'dillalan'

Miracle Kalu mai shekaru 20 a duniya wacce ta yi cikin shege ta haife tare da sayar da diyar a kan N130,000.

Kalu 'yar asalin karamar hukumar Ohafia ce ta jihar Abia. Ta ce rashin kudin kula da halin da ta ke ciki ne yasa ta siyar da jaririyarta mai kwanaki 28 a duniya.

Wacce ake zargin ta ce bayan samun cikin da tayi, saurayinta wanda bata san gidansa ba ya musanta cewa shi yayi cikin.

Asiri ya fara tonuwa ne bayan kama Patrick Mbama mai shekaru 41 da Ogechi Ekwebele mai shekaru 30 da aka yi a Legas.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Legas, Hakeem Odumosu, ya ce an kama su ne yayin da jinjirar ke kuka a motar haya amma wacce ke rike da ita ta kasa shayar da ita. Hakan ya kawo shakku a zuciyar fasinjojin.

Talauci da tsananin rayuwa ce ta sa na sayar da jinjira ta - Mata mai shekaru 20

Talauci da tsananin rayuwa ce ta sa na sayar da jinjira ta - Mata mai shekaru 20. Hoto daga The Nation
Source: Twitter

KU KARANTA: COVID-19: Jerin jihohi 6 da WHO za ta gwada maganin korona a Najeriya

Odumosu ya ce: "Bayan tuhumar ta da aka yi, ta bayyana cewa wasu mata da mijin da basu haihuwa ne suka siya jinjirar."

Kalu, wacce ta zanta da manema labarai, ta ce ita marainiya ce kuma barin makaranta tayi, jaridar The Nation ta wallafa.

Amma kuma, wata majiya daga jami'an tsaro ta bayyana cewa sayar da 'ya'ya halayyar Kalu ce don ba wannan bane karon farko da ta fara haihuwa tana sayar da jariran ba.

Mbama da Ekwebele sun siya jinjirar a kan N130,000 inda suka siyar da ita a kan N150,000.

Okafor, wacce ta siya jinjirar daga karshe, ta ce rashin haihuwa ce ta sa har ta siya jinjirar. "Rashin haihuwa na shekaru 15 ba wasa bane," ta kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel