An Samu Asarar Rai Da Dukiyoyi Kan Rikicin Sarauta a Wata Babbar Jihar Arewa
- Wani rikicin naɗin sarauta da ya ɓarke a jihar Bauchi ya janyo asarar rai da dukiya mai tarin yawa
- A rikicin da ya ɓarke wani dattijo ya kwanta dama yayin da mutane da dama suka samu raunika
- Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin inda tuni har ta ɗauki matakan da suka dace
Jihar Bauchi - Rikicin sarauta a jihar ya janyo asarar ran wani dattijo tare da raunata wasu mutane da dama a cikin ƙaramar Bogoro da ke a jihar Bauchi.
Jaridar Aminiya tace ƴan sanda sun bayyana cewa an kuma kona gidaje da dama waɗanda yawan su aƙalla zai kai aƙalla 64, a rikicin wanda ya ɓarke a daren Asabar, 15 ga watan Afirilun 2023.
Rikicin ya ɓarke a dalilin nadin basaraken ƙauyen Sang, da ke a cikin ƙaramar hukumar ta Bogoro.
Martanin Rundunar Yan Sandan Bauchi
Kakakin rundunar ƴan sandan Jihar Bauchi, Ahmed Alkali, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce wasu da ke adawa da naɗin sarautar da aka yi wa basaraken ne suka yi ta farmakar mutane.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A kalamansa:
"Wasu gungun samari ne daga ɓangarorin a suke adawa da naɗin basaraken kauyen ne suka yi ta kai wa mutane hari, suka ƙona gidaje 64 da babura uku da kuma kadarori na miliyoyin kuɗi."
Kakakin rundunar ƴan sandan ya kuma bayyana cewa an halaka wani dattijo mai shekara 70 a duniya, mai suna Apollos Danlami, sannan aka raunata wani ɗan shekara 65 mai suna Naemiya Bature da kuma wasu da dama a rikicin.
Kakakin ya kuma ce bayan ƴan sanda sun samu kiran gaggawa, sun kai ɗauki zuwa ƙauyen domin dawo da doka da oda, inda a cewar sa yanzu ƙura ta lafa, cewar rahoton The Cable
A cewar kakakin rundunar ƴan sandan jihar ta dauki matakan tabbatar da tsaro a karamar hukumar, sannan Kwamishinan ƴan sandan jihar ya umurci DPO na ƴan sandan Bogoro ya gudanar da ƙwaƙƙwaran bincike kan dalilin tashin hatsaniyar.
Ya kuma ƙara da cewa ana ci gaba da bincike domin cafke masu hannu a rikicin don fuskantar hukunci.
Basarake Ya Kife a Cikin Fada, Ya Rasu a Hanyar Tafiya Masallaci
A wani rahoton na daban kuma, kun ji yadda wani babban basarake ya riga mu gidan gaskiya kan hanyar sa ta zuwa masallaci domin gudanar da ibadah.
Basaraken ya koma ga mahaliccin sa ne yayin da yake tafiya zuwa sallar Magriba.
Asali: Legit.ng