Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani Game da Aisha Binani, Zababbiyar Gwamnan Jihar Adamawa

Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani Game da Aisha Binani, Zababbiyar Gwamnan Jihar Adamawa

  • An ayyana Aisha Binani a matsayin wacce ta lashe zaben gwamnan jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabas
  • Rahotonmu ya bayyana bayanai masu muhimmanci da ya kamata ku sani game da Aisha Dahiru Binani, sanata a Adamawa
  • A bangare guda, INEC ta soke ayyana Binani a matsayin wacce ta kashe zaben, hukumar ta bayyana dalilinta na yin hakan

Jihar Adamawa - A ranar Lahadi 16 Afirilu, 2023 aka ayyana Aisha Dahiru Binani ta jam’iyyar APC a matsayin wacce ta lashe zaben gwmanan jihar Adamawa.

An sanar da hakan ne tare da bayyana cewa, Binani ta lallasa gwamna mai ci a jihar na jam’iyyar PDP, Umaru Fintiri.

To amma meye kuka sani game da Aisha Binani? Kuma meye tarihin siyasa da ayyukanta? Mun tattar muku bayanai game da ita.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa: APC ta lashe kujeru 59, an fadi yawan na PDP, NNPP, LP da SDP

Bayanai game da Aisha Binani
Sanata Aisha Dahiru Binani ta jihar Adamawa | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Binani, zababbiyar gwamna mace ta farko a Najeriya

Sanata Aisha Dahiru Binani ‘yar siyasa ce kuma ‘yar kasuwa, ita ta assasa kamfanin Binani Group da ke gwame da Binani Printing Press da Binani Air da dai sauran hadaka.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta yi karatun difloma a jami’ar Southampton, inda ta karanta Electrical Engineering.

Ta kuma kasance mamba a majalisar wakilai ta kasa, inda ta wakilci mazabar Yola North/Yola Sourth/Girei a karkashin inuwar PDP.

A matakin sanata, ta wakilci Adamawa ta tsakiya a karkashin inuwar jam’iyyar APC, an san ta da kirki da kuma son jama’a.

Ayyukanta na karamci a bayyane suke a jihar Adamawa, wanda hakan ya sanya ta zama fitacciya da suke ji da ita sosai.

Daya daga cikin sanatoci 7 a Najeriya a majalisa ta 9

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 7 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Malamin Makarantar Da Ya Lashe Zaben Gwamnan Kebbi

Binani ta zama sanata ne a 2019 bayan kai ruwa rana. Tana da burin zama gwamna mace ta farko a Najeriyam ba ma a Arewa kadai ba.

A zaben fidda gwamin APC da aka yi a jihar, Aisha Binani ta lallasa ‘yan takara maza shida, ciki har da tsohon shugaban EFCC, Nuhu Ribadu.

A hakan, Aisha Binani na cikin sanatoci bakwai kacan da ake dasu a majalisa ta 9 za ta kare a watan Yuni mai zuwa.

INEC ta soke batun ayyana Aisha Binani a matsayin wacce ta lashe zaben Adamawa

A bangare guda, hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana cewa, ta soke ayyana Aisha Binani a matsayin wacce ta lashe zaben jihar Adamawa.

Wannan na fitowa ne daga wata sanarwar da hukumar ta INEC ta fitar tare da bayyana cewa, baturen zaben da ya sanar da zaben ya saba ka’ida.

Hakazalika, hukumar ta gayyace shi zuwa Abuja domin amsa tambayoyi game da zaben da aka kammala kana ya sanar.

Kara karanta wannan

Fintiri vs Binani: Gwamnan Adamawa ya yi bayani game da kitimurmurar zaben jihar

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.