Jerin Matan Arewa Da Suka Ciri Tuta A Siyasar Najeriya Da Maza Suka Yi Kaka-Gida
- A hankali dai ana samun sauyi a fagen siyasar yankin arewacin Najeriya
- An fara samun mata masu kwarin gwiwar rike manyan mukamai daga arewa
- A yanzu, batun yar takarar gwamnan APC a Jihar Adamawa, Sanata Aisha Dahiru, da aka fi sani da Binani, na kokarin kawo karshen gwamna mai ci
Yadda maza suka mamaye siyasar Najeriya ba sabon abu bane, duk da alkawarin da ake wa manyan kungiyoyin kare mata kan damawa da su a harkokin siyasa da sha'anin mulki.
Duk da wannan kalubale, akwai wasu zakakuran mata da suka dage, suka ja layi don gwada damarsu.
Wadannan mata sun nunawa duniya basirarsu a fannin siyasa, yadda suka samu nasara ta hanyar kwazo da kwarewar aiki.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Muawiyah Yusuf Muye ya tattara wasu jerin mata da suka kawo sauyi a Arewa.
1. Sanata Aisha Dahiru (Binani)
Sanata Aisha Dahiru Binani yar siyasa ce, yar kasuwa, mamallakiyar Binani Group, da ya hadar da Binani Printing Press da Binani Air, da wasu da dama.
Ta mallaki kwalin babbar diploma (HND) a fannin kimiyyar lantarki (Electrical Engineering) daga Jami'ar Southampton. Ta taba wakiltar Yola ta arewa/Yola ta Kudu/Gerei a zauren Majalisar Tarayya.
Kasancewarta Sanata mai wakiltar Adamawa ta Tsakiya kuma yar takarar gwamnan APC, an san ta da yin abin da ya kamata da kyautatawa dan adam. Na sha zama tare da ita lokuta da dama amma bata da girman kai irin na shaharrun mutane.
Ta shimfida manyan ayyukan alheri a Adamawa, abin da ya jawo mata soyayyar mutane.
Sanata Binani ta lashe kujerar sanata a 2019. Ana sa rai za ta iya zama gwamna ta farko ba iya a arewa ba har a Najeriya gaba ki daya, nasarar da za ta zama abar alfahari ga mata ba iya a arewa har a Najeriya dama Afirika baki daya.
2. Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe
Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe ita ce mataimakiyar gwamnan Kaduna. A zaben gwamnan 2019, Gwamna El-Rufai, wanda ke kokarin ganin ya kawo sauyi kan wasu dokoki a gwamnatinsa, da kuma rage karfin kiristocin kudancin Kaduna na neman tikitin Musulmi/Kirista, ya yanke shawarar sanya takararsa a hadari ta hanyar tsayar da Dakta Sabuwa Balarabe a matsayin mataimakiyarsa, wanda ya saba da al'adar arewacin Najeriya na zabar mace a matsayin mataimakiya amma daga karshe anyi nasara.
Ta zama mace ta farko da ta rike irin mukamin daga arewacin Najeriya.
Kamar ni, Dakta Hadiza ta gama Jami'ar Maiduguri, inda ta samu horo a matsayin likitar fida da kwarewar aiki ta sama da shekara 20 a fannin lafiya.
Ta taba rike darakta a sashen kula da lafiyar al'umma a Abuja daga 2014 zuwa 2016, lokacin da Gwamna El-Rufai ya nada ta a matsayin sakatariyar hukumar kula da cigaban kananan asibitoci na Jihar Kaduna; an sake tsayar da ita karo na biyu a matsayin yar takarar mataimakiyar zababben gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani a zaben 2023.
Ta kasance daya daga cikin wanda suka ketare iyaka a mukaman da maza suka mamaye a siyasa.
3. Dakta Ramatu Tijjani Aliyu
Kwararriyar mai tsara birane da ta kammala jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ta shahara a baya bayan nan a siyasar Najeriya.
"The Amazon" kamar yadda magoya bayanta ke kiranta, RTA na da digiri na biyu a fannin gudanar da al'umma da kuma digirin digirgir a fannin ilimin dabarun tsaro daga jami'ar Jihar Nasarawa, da ke Keffi.
Ta na kuma da digirin girmamawa a fannin gudanar da al'umma daga Jami'ar Commonwealth, London, da kuma shaida akan dabarun shugabanci daga kwalejin Abbey, London.
Ta fara shahara a fagen siyasa daga lokacin da ta zama mataimakiyar shugaba (arewa ta tsakiya) a jam'iyyar ANPP a 2008 kafin ta narke, inda daga baya ta rike shugabar mata ta jam'iyyar daga 2010 - 2013.
Bayan an yi hadaka don kafa jam'iyyar APC a 2013. Dakta Ramatu ta zama shugabar mata ta jam'iyyar, mukamin da ta taimaka wa shugaba Buhari don lashe zabe a 2019. Daga baya an nadata ministar Abuja, mukamin da ta rike da kyau.
4. Hadiza Bala Usman
Hadiza Bala Usman ta kammala Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, inda ta samu digirin farko a fannin gudanar da kasuwanci. Ta kammala digiri na biyu a fannin Developmental Studies daga Jami'ar Leeds da ke Ingila.
A matsayinta na tsohuwar shugabar ma'aikatan gwamnan Jihar Kaduna, Mal. El-Rufai, nadinta ya nuna yadda take da matukar kwazo da cancanta. Matakin da ta kai ba abin mamaki ba ne ganin irin mukamin da ta rike a baya a matsayin daya daga cikin wadda suka fi tallata APC a 2015.
Wa'adinta a matsayin babbar daraktar hukumar tashar jiragen ruwa ta Najeriya (NPA) alamu ne na irin yaddar da aka yi da ita. Ta kirkiro sabbin dokoki da za su taimaka wajen sauya fasalin hukumar. Cikin rashin tsaro ta magance kalubalen da ke gabanta ko da zai janyo ta rasa aikin. Kwarewarta ta sanya ta zamo daya daga cikin shugabanni da ake ganin kima kuma ya janyo yan Najeriya da yawa na kaunarta.
A 2023, an nadata a matsayin mataimakiyar shugaba (sashen gudanarwa) na kwamitin kamfen din Tinubu/Shettima. Ta cigaba da kasancewa abar koyi ga mata masu tasowa don kai wa ga nasara a duk al'amuransu.
5. Sanata Binta Masi Garba
Sanata Binta Masi Garba shaharriyar mai rajin kare hakkin mata; ta kammala Polytechnic Kaduna, inda ta samu kwalin babbar diploma ta kasa (HND) a kasuwanci.
Baya ga haka, ta halarci Harvard Kennedy School of Government inda ta samu kwali akan gudanar da dukiyar al'umma. Ta fara aiki a matsayin mai tallace-tallace a jaridar New Nigeria.
An zabe ta a matsayin mai wakiltar Kaduna ta kudu a zauren majalisar kasa a 1999; a lokacin, ita ce mafi kankantar shekaru a majalisar Najeriya.
Ta sake yin takara a zauren majalisar wakilan tarayya a jihar ta Adamawa, mai wakiltar Madagali/Michika, lamarin da ya sanya ta zama yar siyasa ta farko da ta wakilci mabambantan mazabu a majalisar wakilai a lokuta daban-daban.
Asali: Legit.ng