“Mun Shafe Shekaru 10 Muna Soyayya”: Hotunan Kyakkyawar Budurwa Da Ta Amarce Da Amininta Sun Yadu

“Mun Shafe Shekaru 10 Muna Soyayya”: Hotunan Kyakkyawar Budurwa Da Ta Amarce Da Amininta Sun Yadu

  • Wata kyakkyawar budurwa yar Najeriya ta ba da labarin soyayyarta a Twitter bayan ta amarce da sahibinta
  • Matashiyar ta bayyana cewa an haife su a rana daya kuma a shekara daya, a gari guda sannan suka hadu a makaranta daya
  • Abun farin ciki sai suka zama abokai suna da shekaru 13 har sai da suka gano cewa sun fada tarkon son junansu

Wata yar Najeriya mai suna @Tiwalowla a Twitter ta bayyana yadda ta auri mijinta wanda aka haife su a rana daya da ita.

A cewar matashiyar, sun kasance abokan juna tun suna yara sannan suka zama aminai suna da shekaru 13 a duniya.

Saurayi da budurwa na shirin shiga daga ciki
“Mun Shafe Shekaru 10 Muna Soyayya”: Hotunan Kyakkyawar Budurwa Da Ke Shirin Amarcewa Da Amininta Sun Yadu Hoto: @tiwalowla
Asali: Twitter

Kimanin shekaru bayan nan, sai suka gano cewa sun fada tarkon son junansu ne don haka suka ba soyayya damar taka rawar gani a rayuwarsu.

Kara karanta wannan

Daga Tsana Zuwa Soyayya: Magidanci A Social Midiya Ya Bayyana Yadda Budurwar Da Ta Tsane Shi Ta Zama Matarsa

Sun shafe tsawon shekaru 10 suna soyayya har sai da masoyinta ya sanya mata zoben kauna a hannunta inda ya nemi aurenta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalamanta:

"An haife mu a rana daya, shekara daya, a gari daya sannan muka kare a makaranta daya. Mun zama aminai muna da shekaru 13 lokacin da wani malami ya hukuntamu saboda mun cika korafi. Muna da shekaru 18 sai muka gane mun fada tarkon son junanmu sannan muka yanke shawarar ba soyayya dama. Bayan shekaru 10 ya saka mun zobe a hannu."

Jama'a sun yi martani

Thegermandude ta rubuta:

"Ina son irin wannan labarin soyayyar. Ba wai yin aure cikin watanni 3 ba."

DohnDada ya yi martani:

"Da fatan dai kun yi tambayoyi faaa. Kada ya zaman malamar asibiti da ke bakin aiki a wannan rana ta sha barasa kafin ta raba gado bayan haihuwa."

Kara karanta wannan

“Na Zata Zan Yi Aure Ina Da Shekaru 22”: Dirarriyar Budurwa Ta Bayyana Yadda Rayuwarta Ta Sauya Bayan Shekaru a Bidiyo

Yang El ya yi matrani:

"Kai Ubangiji ya dauki lokaci a kan lamarin ku fa, Wannan hadi ne daga sama. Ina fatan wasunmu basu fice daga soyayyar da aka kulla mu da shi tun daga sama ba."

Dattijuwa ta yi tattaki daga Amurka zuwa Najeriya, ta amarce da sahibinta dan saurayi a bidiyo

A wani labarin kuma, wata dattijuwar mata ta cika da farin ciki bayan ta shige daga ciki tare da hadadden saurayinta dan Najeriya.

Matar wacce take mazauniyar Amurka ta shigo jirgi har Najeriya domin hadewa da sahibin nata wanda a yanzu ya zama angonta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng