Wata Dattijuwar Mata Ta Yi Tattaki Daga Amurka Zuwa Najeriya, Ta Yi Wuff Da Matashin Saurayi

Wata Dattijuwar Mata Ta Yi Tattaki Daga Amurka Zuwa Najeriya, Ta Yi Wuff Da Matashin Saurayi

  • Wata dattijuwar mata da ke zama a Amurka ta haddasa cece-kuce bayan bayyanar bidiyonta tana auren wani dan Najeriya
  • Matar, wacce ke cike da farin ciki da tafiyar, ta yi shar da ita a wani hadadden doguwar riga a lokacin aurenta
  • Mutane da dama a sashin sharhi sun taya ta murna yayin da suke fatan hakan zai zamo mafi alkhairi ga ma’auratan

Wata mata a TikTok, @blessedtamma, wacce ke zaune a Amurka, ta yi dan gajeren bidiyo da ke nuna lokacin da ta garzaya Najeriya don auren sahibinta.

Ta dauki bidiyon kanta a cikin jirgin sama yan mintuna kafin su sauka. Yan sakanni a bidiyon, matar ta kasance cikin farin ciki sanye da doguwar rigar amare.

Ma'aurata a wajen shagalin bikinsu
Wata Dattijuwar Mata Ta Yi Tattaki Daga Amurka Zuwa Najeriya, Ta Yi Wuff Da Matashin Saurayi Hoto: @blessedtamma
Asali: TikTok

Shagalin bikin aure me kayatarwa

Wani bangare na bidiyon ya nuno dangin mutumin kewaye da ita yayin bikin aurensu. Dan karamin taro ne amma mai matukar tasiri.

Kara karanta wannan

“Na Zata Zan Yi Aure Ina Da Shekaru 22”: Dirarriyar Budurwa Ta Bayyana Yadda Rayuwarta Ta Sauya Bayan Shekaru a Bidiyo

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wallafar da ta yi, ta bayyana cewa ta yi matukar farin ciki da auren mijin nata.

Mutane da dama sun je sashin sharhi na matar domin taya ma’auratan murna. Wasu sun gargadeta kan fitar da mutumin kasar waje cikin gaggawa.

Kalli bidiyon a kasa:

Bidiyon ya tattara martani fiye da 1200 da ‘likes’ fiye da 9,000.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:

Monica Carter822 ta ce:

“Gaba daya dangin sun kasance a ciki.”

Viv_001 ta ce:

“Da yar Najeriya ce da ba zai yi kuskuren aurenta ba, Ina fatan kana sonta.”

Ariesme84 ta ce:

“Ina tayaki murna!!! Duk abun da za ki yi, kada ki je da shi Amurka. Ki je chan ki zauna na akalla rabin shekara.”

queen stella ta ce:

“idan har da gaske ne toh Ina fatan ba za ki yi dansani ba.”

Kara karanta wannan

"Girmanki Ne": Bidiyon Yadda Matar Aure Ta Ki Yarda Ta Shiga Gaban Motar Mijinta Don Karrama Surukarta Ya Tsuma Zukata

Neptina ta ce:

“Yarinya...za ki ji dadin daren aure mai kyau. Allah ya yi albarka.”

lazorusTheDan ya ce:

“Biza wani irin abu ne gaba daya dangin Za su tafi lol.”

Matar aure ta mutunta surukarta wajen shiga mota a bidiyo

A wani labarin kuma, wata matashiyar mata ta karramawa uwar mijinta yayin da suka zo fita unguwa tare, ta hakura ta bar mata gaban motar danta don ta zauna a ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng