Yan Ta'adda 15 Sun Sheka Barzahu Yayin da Sojoji Suka Dakile Hari a Zamfara
- Sojojin Najeriya da haɗin guiwar yan banga sun yi nasarar dakile harin yan bindiga a kauyukan jihar Zamfara
- Mazauna sun ce 'yan bindiga sun shiga garuruwansu ranar Laraba amma Sojoji suka tarbe su, suka kashe 15
- Kwamandan Operation Hadarin Daji ya yaba da jajircewar sojoji kana ya roki Zamfarawa su rika basu bayanai
Zamfara - 'Yan bindigan daji 15 da suka yi mubaya'a ga ƙasurgumin ɗan ta'addan nan, Ɗankarami, sun gamu da ajalinsu a hannun Sojojin rundunar Operation Hadarin Daji a jihar Zamfara.
Rahoton Channels tv ya nuna cewa daga cikin waɗanda Sojoji suka raba da numfashi har da babban kwamandan Ɗankarami.
Yan ta'addan, waɗanda suka yi yunkurin kai hari kan mutane a kauyukan Gidan Danjimma da Kirifada a yankin ƙaramar hukumar Birnin Magaji, sun kwashi kashinsu a hannu.
Dakaru rundunar soji da haɗin guiwa Yan banga ne suka samu nasarar dakile harin 'yan bindigan a ranar Laraba, kuma suka tura da yawa lahira.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Zuwa yanzun da muke haɗa muku rahoto, majiyoyi da dama sun ce 'yan bindiga sun taru da yawa suna jana'izar waɗanda aka kashe musu a Maƙabartar kauyen Mai Tsaba, ƙaramar hukumar Zurmi.
Yadda lamarin ya faru a kauyukan 2
Wani ɗan kauyen Kirifaɗa da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce 'yan fashin dajin sun kutsa ƙauyukansu ranar Laraba, amma Sojoji suka kawo ɗauki har suka sheƙe 15.
Ya ƙara da cewa adadi mai na maharan sun jikkata har da wanda ake kira 'Ba sulhu' ɗaya daga cikin mayaƙan da Ɗankarami ke ji da su.
A ɗaya bangaren kuma Dakarun soji biyu da yan banga huɗu sun ji raunuka daban-daban yayin musayar wuta da yan binidgan amma babu wanda ya mutu.
Da yake tsokaci, kwamandan rundunar haɗin guiwa ta Operation Hadarin Daji a arewa maso yamma, Manjo Janar Godwin Mutkut, ya yaba da namijin kokarin sojojin.
Kwamandan ya kuma yi kira ga mazauna jihar Zamfara da su ci gaba da baiwa hukumomin tsaro bayanai a kan lokaci a kokarinsu na dawo da zaman lafiya.
Jami'in Kotun Shari'ar Musulunci a Neja Ya Mutu
A wani labarin kuma kun ji cewa Jami'in Kotun Shari'ar Musulunci a Neja Ya Mutu a Hannun Yan Bindiga
An ce yan bindigan sun harbe Rijistaran Kotun Musulunci da sauran mutanen da suka sace yayin da jami'an tsaro suka matsa musu lamba domin ceton mutanen.
Wani mazaunin yankin da abun ya faru a jihar Neja ya ce har yanzu ana kokarin ɗauko gawar mutanen don musu Jana'iza.
Asali: Legit.ng