Dalibar Ajin Farko A Kwaleji Ta Yanke Jiki A Aji Ta Yi Bankwana Da Duniya Ana Kwana Daya Bikin Rantsar Da Su

Dalibar Ajin Farko A Kwaleji Ta Yanke Jiki A Aji Ta Yi Bankwana Da Duniya Ana Kwana Daya Bikin Rantsar Da Su

  • Daliba ta fadi ana tsakiyar darasi ta kuma mutu ana saura kwana daya bikin rantsar da ita a matsayin sabuwar daliba
  • Mahaifin yarinyar ya bayyana cewa yar sa lafiyarta kalau kuma sun tattauna abubuwa da dama kafin ya rakata ta hau mota zuwa makaranta
  • Hukumar makaranta ta bayyana yadda dalibai suka yi jimamin mutuwar abokiyar karatunsu a wajen taron bikin rantsar da sababbin daliban

Jihar Kwara - Wata sabuwar da a kwalejin ilimi ta Jihar Kwara, Amina Akanke Tajudeen, ta yanke jiki ana tsaka da darasi ta mutu, Vanguard ta rahoto.

Lamarin, da wakilin majiyarmu ya ruwaito, ya faru da misalin 1:30 na ranar Laraba jim kadan bayan marigayar ta karbi rigar ranar rantsuwar sabbin dalibai da aka shirya gudanarwa ranar Alhamis ta kuma dawo ajin.

Kara karanta wannan

Yan Fashi Da Makami Sun Kai Mummunan Hari Kasuwar Ogun Da Tsakar Rana, Sun Kashe Wani Dan Kasuwa

Daily Trust
Dalibar Kwaleji A Kwara Ta Yanke Jiki Ta Yi Bankwana Da Duniya. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

An garzaya da daliban asibiti bayan ta fadi

Wani babban malamin makarantar da ya magantu a kan lamarin wanda ya boye sunansa, ya ce an yi gaggawar kai marigayar asibitin makaranta bayan ta fadi ana tsaka da darasi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata dalibar jinya da ta duba dalibar ta bayyana cewa dalibar ta mutu lokacin da aka kawo ta asibitin amma an kai ta babban asibitin Illorin don kiyaye faruwar zanga zangar dalibai.

Daga bisani an dawo da ita makabartar Osere, inda aka binne ta.

Da yake bayani bayan binne ta, mahaifin marigayar, ya ce:

"Ba ta nuna alamun rashin lafiya ba. Mun yi doguwar hira da ita akan abubuwa da dama kafin in rakata ta hau mota zuwa makaranta."

Mai magana da yawun Kwalejin ta tabbatar da rasuwar Amina

Mai magana da yawun makarantar, Mrs Abibat Zubair, wadda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta shaida wa Daily Trust cewa dalibar na karantar Music/Yoruba, ta kara da cewa an yi jimamin mutuwarta lokacin bikin rantsar da dalibai.

Kara karanta wannan

Na Shiga Uku: Nasarar APC Ta Jefa Ni Cikin Hadari Inji Tsohuwar Mataimakiyar Gwamnar Legas

"Shugaban kwalejin ya ziyarci iyayenta jiya (Laraba) don yi musu ta'aziyya kuma an yi jimamin mutuwarta yau tare da dalibai yayin bikin rantsar da dalibai," in ji jami'ar huldar.

Da aka bibiyi shafinta na Facebook ya nuna cewa yau (Alhamis) zai kasance ranar murnar haihuwarta, daidai da ranar bikin rantsar da ita a matsayin sabuwar daliba.

Wani rubutu da abokin karatunta daga sashen koyar turanci, Abdulhameed Nafiu Ishola ya ce:

"Mutuwa mai zuwa ba sanarwa. Kina da kirki da kamun kai kamar tantabara, nutsatstsiya mai kuma mai tarbiya. Kina murmushi kan duk abin da aka fada miki kuma kinyi alkawarin zaki tsaya tare da mu ranar bikin tunawa da haihuwarki yau (Alhamis). Amma kin bar mu cikin bakin ciki."

DPO ya yanke jiki ya fadi a ofis, ya yi bankwana da duniya

A wani rahoton kun ji cewa DPO na yan sanda a Legas, SP Mojeed Salami ya riga mu gidan gaskiya bayan yanke jiki ya fadi a ofishinsa.

Kara karanta wannan

"Girmanki Ne": Bidiyon Yadda Matar Aure Ta Ki Yarda Ta Shiga Gaban Motar Mijinta Don Karrama Surukarta Ya Tsuma Zukata

Ya dawo daga ofishinsa ne sai ya kira yaronsa na ofis ya fada masa baya jin jikinsa yadda ya saba, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164