Gwamna Ortom Na Son Gwamnatin Buhari Ta Dage Yin Wani Kidaya, Ya Bada Dalili

Gwamna Ortom Na Son Gwamnatin Buhari Ta Dage Yin Wani Kidaya, Ya Bada Dalili

  • Gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom, ya bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar da aikin kidaya da ta shirya gudanarwa a wata mai kamawa
  • Ortom ya ce akwai bukatar a samar da tsaro da zai ba wa yan gudun hijira damar komawa yankunansu kafin gudanar da kidayar
  • Ortom ya ce akwai wata boyayyiyar manufa da ke boye cikin shirin kidayar

Jihar Benue - Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue, a ranar Alhamis, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ya dage yin aikin kidiya yan kasa da ake shirin yi a watan Mayu, Daily Trust ta rahoto.

Ortom ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya tarbi tawagar kungiyar Middle Belt karkashin jagorancin shugabanta, Dakta Bitrus Pogu, a Gidan Gwamnati a Makurdi.

Samuel Ortom
Gwamna Ortom Ya Bukaci Gwamnatin Buhari Ta Dage Yin Kidaya, Ya Bada Dalili. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Gwamnan ya ce mutanen jiharsa da dama suna sansanin yan gudun hijira kuma ba za a kirga su ba domin akwai bukatar su koma garuruwansu kafin su samu damar shiga kidiyar.

Kara karanta wannan

"Ka Yi Hakuri," Gwamnatin Burtaniya Ta Aike da Sako Mai Muhimmanci Ga Peter Obi Kan Abinda Ya Faru

Ya ce kafin a gudanar da kidaya, dole ne gwamnatin tarayya ta tabbatar da wadataccen tsaro don yan gudun hijira a Benue da sauran wurare a kasar nan su iya komawa gida don a kirga su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina so in ce ya kamata gwamnatin tarayya ta dakatar da maganar kidaya saboda kamar akwai wata manufa. Don haka, sai an samar da tsaro ga duk yan gudun hijira don su koma garuruwansu don bada damar kirga su a mahaifarsu. Saboda abun da na fahimta shi ne hukumar kidaya za ta kirga wanda ke gidajensu," in ji shi.

Ortom ya kara da cewa akwai rashin adalci da yawa, wariya da kabilanci da ke damun kasar nan kuma akwai bukatar shugabanni da mutane su gyara kafin a samu cigaba a kasar.

Jawabin shugaban Middle Belt Forum, Bitus Pogu

Kara karanta wannan

Gwamna Gandije ya caba, majalisa ta amince da kudurinsa kan masarautun Kano

Da ya ke magana, shugaban Middle Belt Forum, Dakta Bitrus Pogu, ya goyi bayan Gwamna Ortom, ya kuma roki gwamnatin tarayya da ta dakatar da shirin kidayar saboda yana ganin, "akwai boyayyiyar manufa."

Pogu ya kuma koka kan yadda yan fashin daji ke cigaba da kashe mutane a yankin na Middle Belt.

Ya kara da cewa mutanen mutanen Middle Belt, "ba za su bari a siyar yankin mu ga kowa ba. Ba wani yankin mu da zamu bari siyarwa wani. Ba zamu bari ba. Ba za mu bari haka ta faru ba. Kasarmu ce gadon mu."

Ba ka riga ka dare kan kujerar gwamnan Kano ba, Ganduje ya gargadi Abba Kabir Yusuf

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Kano mai barin gado Abdullahi Ganduje ya ja kunnen Abba Kabir Yusuf, gwamna mai jiran gado ya dena saka baki kan mulkin jihar a yanzu.

Kara karanta wannan

Lambar Ministoci 2 Ya Fito da ‘Yan Majalisa Ke Binciken Satar Gangunan Mai Miliyan 48

Gandujen ya tunatar da zababben gwamnan cewa shine gwamnan Kano har zuwa ranar 29 ga watan Mayu don haka ba shi da ikon bada umurni a abin da ke hurumin gwamnati ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164