Gwamnatin Burtaniya Ta Baiwa Peter Obi Hakuri Kan Tsare Shi Ba Kan Ka'ida Ba

Gwamnatin Burtaniya Ta Baiwa Peter Obi Hakuri Kan Tsare Shi Ba Kan Ka'ida Ba

  • Gwamnatin Butaniya ta nemi yafiyar Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar LP A zaben 25 ga watan Fabrairu, 2023
  • A wata sanarwa da Labour Partyta wallafa a shafinta a yanar gizo, gwmanatin UK ta nemi afuwar Obi kai tsaye
  • Jam'iyyar ta yi ikirarin gwamnatin Burtaniya ta ce tsare Peter Obi lokacin shagalin Sita ba daidai bane

Abuja - Jam'iyyar Labour Party (LP) ta yi ikirarin cewa gwamnatin kasar Burtaniya ta aike da sakon neman afuwa ga Peter Obi, ɗan takarar shugaban kasa a zaben 25 ga watan Fabrairu, 2023.

A sanarwan da LP ta wallafa a shafinta na yanar gizo, jami'in hukumar shige da fice ta ƙasar Birtaniya ya amince cewa sun tsare Obi bisa kuskure yayin neman wani da ya yi basaja.

Peter Obi.
Gwamnatin Burtaniya Ta Baiwa Peter Obi Hakuri Kan Tsare Shi Ba Kan Ka'ida Ba Hoto: Peter Obi
Asali: Facebook

A cewar jami'in sun yi kuskuren tsare Peter Obi ne yayin da suke neman wani da ya yi basaja da sunan Obi bisa aikata laifin karyan takardu da satar bayanai.

Kara karanta wannan

Gwamna Ortom Na Son Gwamnatin Buhari Ta Dage Yin Wani Kidaya, Ya Bada Dalili

Haka nan LP ta yi ikirarin cewa gwamnatin UK watau Burtaniya ta bayyana cewa abinda aka yi wa Mista Obi, "Bai dace ba ko kaɗan," kuma ta nemi afuwa daga wurinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jam'iyyar ta ƙara da cewa hukumar shige da fice fa ƙasar Burtaniya, ta nemi yafiya inda ta ce, "A zahirin gaskiya abinda jami'an hukumar shige da fice suka aikata ba daidai bane, kuma mun ba da hakuri."

Idan baku manta ba, jami'ai sun damƙe wa Obi takardar izinin tsare shi yayin da yake kan layi domin bin ƙa'idojin filayen jirgin sama kafin daga bisani aka umarci ya koma gefe.

Lokacin ɗa yake kan layi domin bin matakai da dokokin filin jirgi, ba zato jami'an hukumar shige da fice suka zo kansa, suka ba shi takardar neman tsare shi, daga baya suka umarci ya koma gefe.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Wani Babban Jami'in Kotun Musulunci Ya Rasu Ta Hanya Mai Ban Tausayi a Watan Azumi

A cewa kakakin kamfen LP, Diran Onifade, an yi wa Obi tambayoyi lokacin da yake tsare kan wani da shiga Landan da bayanai iri ɗaya da nasa.

Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Tsohon Shugaban 3SC, Baba Lankondaro, Ya Mutu

A wani labarin kuma Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Tsohon Shugaban 3SC Ya Rigamu Gidan Gaskiya

Tsohon shugaban ƙumgiyar kwallon kafa ta 3SC kuma wanda ake ma kallon mafi daɗewa yana goyon bayan kwallon ƙafa a Najeriya ya kwanta dama yana da shekaru 111.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262