Lambar Ministoci 2 Ya Fito da ‘Yan Majalisa Ke Binciken Satar Gangunan Mai Miliyan 48

Lambar Ministoci 2 Ya Fito da ‘Yan Majalisa Ke Binciken Satar Gangunan Mai Miliyan 48

  • An kafa wani kwamitin amajalisar wakilai da yake bincike kan wasu kudi da ake zargin sun yi kafa
  • Mark Tersee Gbillah ya ce wasu jami’an gwamnati sun karbi kudin da ba su shiga asusun gwamnati ba
  • ‘Yan majalisar tarayya sun aika sammaci ga SGF, AGF da Ministar kudi domin a iya jin ta bakinsu

Abuja - Kwamitin majalisar wakilan tarayya da ke bincike a kan zargin sace kudin da aka samu wajen saida mai ya aikawa wasu Ministoci sammaci.

Wani rahoto na Daily Trust ya ce kwamitin yana neman ganin Ministar tattalin arziki, Zainab Ahmed da sakataren gwamnatin kasa, Boss Mustapha.

Sammacin ya shafi Abubakar Malami wanda shi Ministan shari’ar kuma lauyan gwamnatin tarayya. Ana sa ran dukkansu za su bayyana a majalisa.

Shugaban kwamitin binciken, Hon. Mark Tersee Gbillah ya bada wannan umarni bayan kwamitin da yake jagoranta ya cigaba da zama a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Gwamnoni Sun Hango Matsala a Majalisa, Sun Nemi a Dauki Matakin Gaggawa a APC

An saida gangunan mai a boye

Mark Tersee Gbillah su na bincike a kan zargin saidawa kasar Sin wasu ganguna miliyan 48 na danyen mai da suka ce an yi ba tare da bin ka’ida ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahoton ya ce wasu jami'ai suka fallasa abin da ake zargin ya faru, sai majalisa ta shiga bincike.

'Yan majalisa
'Yan majalisa a wani zama Hoto: @HouseNgr
Asali: Twitter

Ana neman SGF, AGF, Ahmed

Ana kokarin sanin rawar da ma’aikatar tattalin arziki da sauran hukumomin harkar kudi suka taka wajen yin barazana ga wadanda suka tona badakalar.

Gbillah yake cewa kwamitinsa ya na so ya ji daga bakin Ministan shari’a da sakataren gwamnatin tarayya, amma ba su samu halartar zaman ba.

Premium Times ta rahoto ‘dan majalisar yana kokawa kan kin bayyanar jami’an gwamnatin a gabansu, don haka ya tura masu sammaci a hukumance.

Zargin da ake yi shi ne Ministan shari’a ya ce Ministan tattalin arziki ta na biyan kudi ba tare da bin abin da doka ta ce ba ga wadanda suka fasa kwai.

Kara karanta wannan

Tsirarun Mutane Sun Tashi da Naira Biliyan 20 a Kwamitocin Shugaban Kasa a Shekara 8

Haka zalika ana tuhumar AGF da hannu wajen karbar wasu kudi a wajen Najeriya, ba a nan abin ya tsaya ba, majalisar ta ce kudin ba su shiga baitul-mali ba.

A kan binciken mai, ana sauraon rahoton NURC, NEITI, kamfoni da bayanin Akanta Janar.

Za ayi zama da Tinubu

Kwanaki kadan suka rage a rantsar da sabuwar majalisar tarayya, amma APC na neman shiga cikin rudani kamar yadda wani rahotonmu ya bayyana.

Sanatoci da ‘yan majalisa daga kowane bangare sun tsaya takara, jam’iyya ta ki raba gardama. Ana sa rai ayi zama tsakanin Gwamnoni da shugabannin APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng