Peter Obi Na Son Tada Hankali a Najeriya, Dattawan Arewa Sun Tura Masa Sakon Gargadi

Peter Obi Na Son Tada Hankali a Najeriya, Dattawan Arewa Sun Tura Masa Sakon Gargadi

  • Gamayyar kungiyar dattawan Arewa ta yi waje da yunkurin Peter Obi na son a kwace nasarar Bola Ahmad Tinubu
  • Kungiyar ta ce, akwai alamu da ke nuna Peter Obi na son haifar tarzomar juyin mulki a kasar nan duba da dabi’unsa bayan zabe
  • A baya, gwamnan APC ya ce, babu mahalukin da ya isa ya hana rantsar da Bola Ahmad Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa

Jihar Kaduna - Wata gamayyar kungiyar dattawan Arewa ta ce dabi’a da tsarin da Peter Obi dan takarar jam’iyyar Labour ke nunawa a martaninsa na bayan zaben shugaban kasa sun sabawa ka’ida ta hankali da tsarin mulkin kasar nan.

A rahoton Daily Trust, dattawan sun gargadiObi da sauran ‘yan siyasa da su daina tofa kalaman da ka iya tada hankalin jama’a da hada fada tsakanin al’umma.

Kara karanta wannan

Ku rabu dashi: Peter Obi ya tafi kotu ya shirga karya game da zabe, INEC ta yi martani

A cewar dattawan Arewa, kalaman Peter Obi da magoya bayansa na iya haifar da aukuwar irin juyin mulkin da sojoji suka yi a 1966, inda aka kashe shugabannin yankin Arewa masu daraja.

Dattawan Arewa sun gargadi Peter Obi
Peter Obi, dan takarar shugaban kasan da aka gano ya hada kai da kiristoci | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Peter Obi ya yi kamfen raba kan al’umma da addinai

Dattawan Arewa sun ci gaba da cewa, a bayyane yake cewa Obi ya yi kamfen raba kan addinai a babban zaben da aka kamala na bana, rahoton The Nation.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Suleiman Usman Jere, shugaban gamayyar ne ya bayyana hakan a wata sanarwar da ya fitar bayan taron kungiyar a Arewa House da ke Kaduna a ranar Talata 11 ga watan Afrilu.

Sun nuna damuwar cewa, dan takarar shugaban kasan Labour na ci gaba da nuna wasu halaye na rashin bin tsarin dimokradiyya da ka iya haifar rabuwar kan jama'a da kuma barazana ga makomar dimokuradiyyar Najeriya.

Kara karanta wannan

Ana Saura Kwanaki 50 Ya Bar Aso Rock, An Yi Karar Shugaba Buhari da NBC a Kotu

Idan baku manta ba, tun bayan kammala zaben shugaban kasa na bana ne Peter Obi yace bai amince da sakamakon ba, zai kalubalanci sakamakon a gaban kotu.

Babu mahalukin da zai iya dakatar da rantsar da Tinubu

Sai dai, a wani labarin na daban, gwamnan jihar Ebonyi ya bayyana cewa, duk duniyar nan babu mai iya hana rantsar da Bola Tinubu a matsayin shugaban Najeriya.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin wasu jiga-jigan siyasar jihar, ciki har da sabon zababben gwamnan jihar.

Hakazalika, ya bayyana aniyarsa ta gaje kujerar Ahmad Lawal a majalisar dattawa, inda yace ya jima yana mafarkin zama shugaban majalisa ta 10.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.