Shugaba Buhari ya isa Birnin Madina, Ya Yi Sallah a Masallacin Annabi
- Shugaba Muhammadu Buhari ya isa birnin Madinah da ke kasar Saudiyya inda ya kai ziyarar aiki
- Buhari ya ziyarci Masallacin Annabi inda ya yi sallah a cikinta sannan ya ziyarci kabarin Annabi da sahabbansa
- Shugaban Najeriyan ya samu kyakkyawar tarba daga wajen wasu jami'ai a kofar shiga masallacin Annabi
- Saudiyya - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa birnin Madinah, kasar Saudiyya domin fara ziyarar aiki na tsawon kwanaki takwas, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Jirgin da ya dauki shugaban kasar da wasu hadimansa ya bar filin jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe Abuja da misalin karfe 9:10 na safiyar Talata.
Ya kuma isa filin jirgin saman kasa da kasa na Yarima Mohammed Bin Abdulaziz da ke birnin Madinah da misalin karfe 5:00 na yamma.
A wata sanarwa da ya saki a ranar Talata, 11 ga watan Afrilu, babban mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin labarai, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa da isarsa kasar, ya samu tarba daga mataimakin gwamna Sa’ud Khalid Al-Faisal.
Buhari ya ziyarci masallacin Annabi
Kakakin shugaban kasar ya ce Buhari ya kai ziyara da kuma yin sallah a masallacin Annabi a yammacin yau sannan ya ziyarci kabarin Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da sahabbansa biyu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya kara da cewat shugaban kasar ya samu tarba daga wasu jami'ai a kofar shiga masallacin Annabi, rahoton Vanguard.
Tinubu ya soke tafiyarsa zuwa Landan da Saudiyya don yin Umarah
A wani labarin kuma, mun ji cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zababben shugaban kasa ya fasa zarcewa birnin Landan da kasar Saudiyya don yin aikin Umarah daga kasar Paris.
An tattaro cewa hakan baya rasa nasaba da wutar rikicin da ke shirin kunno kai a jam'iyyar APC saboda fafutukar zababbun yan majalisar tarayya da ke neman shugabancin majalisar ta 10.
Wata majiya a sansanin zabababben shugaban kasar ta bayyana cewa ana sanya ran Bola Tinubu zai yi tsare-tsaren kan yadda bikin rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu za ta kasance hadi da magance matsalar shugabancin majalisar a tsakanin masu takarar mukaman majalisar tarayyar.
Asali: Legit.ng