Kotun Kano Ta Umarci a Sake Sake Turawa Dauda Kahuta Rarara Takardar Sammaci
- Kotun jihar Kano ta sake ba da umarnin a kai wa Rarara takardar sammaci kan ya bayyana gabanta
- Wannan na zuwa ne bayan karar da aka shigar game da siyan wayoyi da ya yi amma ya gaza biyan kudin
- A baya, an manna takardar sammacin a gidan Rarara da ke Zoo Road, amma ba a samu ya zo gaban kotun ba
Jihar Kano - Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Rijiyar Zaki karkashin jagorancin Mai Shari’a Halhalatul Khuza’i Zakariyya a Kano ta ba da umarnin a sake kai sammaci ga fitaccen mawaki Dauda Kahutu Rarara, bisa rashin bayyanarsa a gaban kotun.
Ana tuhumar Rarara ne da kin biyan kudin wayoyin da suka kai N10,300,000 da ya karba ya raba wa mutane daga hannun wani dan kasuwa, Muhammad Ma’aji, Daily Trust ta ruwaito.
Lauyan mai shigar da kara, Barista I. Imam, ya shaida wa kotun cewa Rarara bai mutunta girma da sammacin kotun ba, don haka ya bukaci a ba da umarnin kama shi.
Sai dai Imam ya shaida wa kotun cewa bai da tabbacin ko takardar sammacin da aka ba da a kai wa Rarara ta isa gare shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shin an kai wa Rarara takardar sammaci?
Daga nan ne kotun ta tambayi masinjanta, Isma’il Zuhudu ko ya kai takardar sammacin, inda ya tabbatar da cewa ya manna ta a kofar gidan Rarara kamar yadda kotu ta umarce shi ya yi saboda ganin Rarara ya gagara balle ya bashi hannu-da-hannu.
Alkalin kotun, ya ce tunda yin farko ne, kotu za ta yi watsi da batun umarnin kamun, amma dai a sake tura masa takardar sammacin.
A wannan karon, mai shari’a ya ce a kai wa Rarara sammacin a hannu, ko kuma a manna a gidansa da ke titin Zoo Road sannan a buga a kafafen yada labarai da dai sauransu.
Don haka ya dage sauraron karar zuwa ranar 13 ga Afrilu don sauraran zuwa Rarara da kuma jin yadda za ta kaya.
An yi cece-kuce bayan da aka kama wasu 'yan sandan da ke bin bayan Rarara masu ba shi tsaro saboda wasu dalilai.
‘Yan daba sun cinnawa gidan Rarara wuta a Kano
A wani labarin, kun ji yadda tsagerun ‘yan daba suka bankawa gidan Rarara wuta a jihar Kano bayan zabe.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rikici ya barke bayan sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar.
An ruwaito cewa, an kama wasu da ake zargin suna da hannu a wannan barnar da bata dace ba.
Asali: Legit.ng