Tashin Hankali Yayin Da ’Yan Bindiga Suka Hallaka Jigon APC Mai Fada a Ji a Jihar Delta
- Wasu tsagerun ‘yan bindiga sun hallaka wani jigon jam’iyyar APC a jihar Delta da ke Kudancin Najeriya
- Majiya ta bayyana irin jajircewar wannan jigon kafin daga bisani wasu tsageru suka hallaka shi haka siddan
- Ya zuwa yanzu an kama mutum uku da ake zargi da hannu a kisan, ana kuma ci gaba da bincike a kai
Jihar Delta - Wasu ‘yan bindigan da ake zargin hayarsu aka yi musamman don aikata kisa sun yi hallaka wani jigon jam’iyyar APC, Sylvester Efeurhobo a jihar Delta.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, an harbe jigon na APC ne inda nan take ya mutu a lokacin da ‘yan ta’addan suka kutsa gidansa da ke Agbarho da ke karamar hukumar Ughelli ta Arewa a jihar.
An kuma tattaro cewa, mamacin ya kasance shugaban wata tawagar goyon bayan jam’iyyar APC mai suna Achievers Group dake Agbarho.
Yadda kisan ya auku
Majiya ta bayyana cewa, ana yiwa wannan mamacin kallon jajirtaccen dan jam’iyya kuma dan uwa kana uba; kashin baya gareta a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tuni masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar suka yi kira ga jami’an tsaro da su tabbatar da kamo mashekan tare da hukunta su.
Shugabannin jam’iyyar:
“Ya kamata a hukunta wadanda suka aikata kisan, a daidai lokacin da muke ci gaba da jimamin rashin.”
Martanin ‘yan sanda game da kisan
A lokacin da aka tuntube shi, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe ya tabbatar da kisan Sylvester, Naija News ta ruwaito.
Ya kuma bayyana cewa, an kama mutum uku da ake zargin suna da hannu a kisan, ana ci gaba da bincikarsu kan lamarin.
A cewarsa:
“Tabbas, muna ci gaba da bincke. Ya zuwa yanzu, an kama mutum uku da ake zargi da hannu a kisan.”
An hallaka ‘yan bindiga 2 a jihar Zamfara
A wani labarin, kun ji yadda aka hallaka wasu tsagerun ‘yan bindiga a lokacin da suka kai wani hari a jihar Zamfara.
Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, nan take ‘yan sanda suka sheke tsagerun biyu tare da raunata wasu da yawa.
Jihar Zamfara na daya daga jihohin da ake yawan fama da matsalar tsaro, musamman ‘yan bindiga masu sace mutane don neman kudin fansa.
Asali: Legit.ng