Tirkashi: An Hana Shugaban Kamfanin Jirgin Saman Arik Air Shiga Cikin Harabar Kamfanin

Tirkashi: An Hana Shugaban Kamfanin Jirgin Saman Arik Air Shiga Cikin Harabar Kamfanin

  • An tayar da jijiyoyin wuya yayin da aka hana shugaban kamfanin jirgin sama na Arik Air daga shiga cikin kamfanin
  • Jami'an tsaron da ke bakin aiki a lokacin ne dai suka tubure suka ce sam ba za su bari ya shiga ba
  • Sun bayyana cewa sun samu umurni ne daga sama domin hana shugaban shiga cikin harabar kamfanin

Legas- An samu ƴar ƙaramar hatsaniya a hedikwatar kamfanin jirgin sama na Arik Air, da ke a filin tashi da saukar jiragen sama na ƙasa da ƙasa na Murtala Muhammed a birnin Legas, lokacin da aka hana shugaban kamfanin shiga ciki.

Shugaban kamfanin Cif Johnson Arumemi-Ikhide, ya iso harabar kamfanin tare da wasu hadiman sa domin bin umurnin wata kotu da ta ba shi damar shiga cikin harabar kamfanin, cewar rahoton Daily Trust

Kara karanta wannan

Tsirarun Mutane Sun Tashi da Naira Biliyan 20 a Kwamitocin Shugaban Kasa a Shekara 8

An hana shugaban kamfanin Arik Air shiga kamfanin
Shugaban kamfanin Arik Air a wajen wani taro Hoto: Guardian.com
Asali: UGC

Sai dai, jami'an tsaron da ke aiki a lokacin sun dakatar da shi a ƙofar shiga cikin kamfanin.

Shugaban jami'an tsaron kamfanin jirgin saman na Arik Air, mai suna D Tom-West, ya ce an bashi umurni daga sama kada ya bar shi ya shiga cikin harabar kamfanin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A gardamar da ta ɓarke a tsakanin su, Tom-West ya bayyana cewa umurnin na sama da shi kawai yake bi.

A kalamansa:

“Manaja ya bayar da umurnin kada a bari ka shiga. Bani da wata masaniya kan hukuncin kotu. Ba zamu iya bari ka shiga cikin kamfanin ba. Wannan shine umurnin da aka bamu daga sama."
"Ku yi haƙuri na bar ku a cikin zafin rana. Mun samu umurnin kada mu bari ku shiga. Dole na yi biyayya ga umurnin shugabana na sama da ni"

Shugaban na Arik ya gaza samun ikon shiga harabar

Kara karanta wannan

Madallah: Wata kungiya ta rabawa talakawa 750 kayan abinci a wata jihar Arewa

Arumemi-Ikhide ya gayawa Tom-West cewa ba ya zo wajen bane domin takalar faɗa ko tayar da rikici ba, sai domin bin umurnin kotu wanda ya bashi damar shiga cikin harabar kamfanin.

Ya bayyana cewa ya yi mamaki matuƙa da aka hana shi shiga cikin harabar kamfanin.

Daga ƙarshe shugaban ya haƙura ya bar wajen inda ya wuce zuwa ofishin ƴan sanda na ɓangaren jiragen sama na cikin gida na filin jirgin domin rubuta abinda ya wakana.

Yace zai tuntuɓi lauyoyin sa waɗanda za su cigaba da tafiyar da ragamar daga inda ya tsaya.

Rigima Ta Kunno Kai Tsakanin Gwamna Mai Barin Gado Da Magajin Sa a Benue

A wani labarin na daban kuma, rikici ya kunno kai tsakanin gwamna mai barin gado da magajin sa a jihar Benue.

Rikcin na su dai ya samo asali ne bayan gwamna Ortom ya fara shirin aikewa da wani sabon ƙudiri a gaban majalisar dokokin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng