An Kunno Wa Fitaccen Ministan Buhari Wuta, Ana Neman Gwamnatin Tarayya Ta Cafke Shi

An Kunno Wa Fitaccen Ministan Buhari Wuta, Ana Neman Gwamnatin Tarayya Ta Cafke Shi

  • Wani dattijon ƙasa Cif Edwin Clark ya nemi Antoni Janar na tarayya da ya yi caraf da ministan watsa labarai na tarayya
  • Edwin Clark ya bayyana cewa Lai Mohammed yana jifar Peter Obi da ƙarairayi marasa tushe balle makama
  • Ya zargi Lai Mohammed da yin amfani da muƙamin sa na minista ta hanyar da bata dace ba

Abuja- Tsohon Kwamishinan Watsa Labarai na Tarayya, Cif Edwin Clark, ya yi kira ga Antoni Janar na Tarayya da ya fara tuhumar Ministan Watsa Labarai da Al'adu, Lai Mohammed, cikin gaggawa.

Cif Edwin Clark yana zargin Lai Mohammed da yaɗa ƙarairayi akan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, a gida da wajen Najeriya, cewar rahoton Tribune.

An yi kira da a cafke Lai Mohammed
Ministan watsa labarai, Lai Mohammed Hoto: Sunnewsonline.com
Asali: UGC

Dattijon a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, ya bayyana cewa ministan a maimakon yayi ƙoƙarin haɗa kan ƴan ƙasar nan kamar yadda aikin sa ya nuna, ya koma yana kalamai waɗanda za su iya kawo ruɗani, rahoton Sunnewsonline

Kara karanta wannan

Ashsha: Yadda Aka Babbake Wani Matashi Kan Zargin Satar Wayar Android, Ya Kone Kurmus

Ya kuma koka kan cewa ministan ya nuna wasu ɗabi'u waɗanda bai kamata ace mutum mai muƙami irin nasa ya nuna su ba, inda yayi nuni da yadda yake amfani da hukumar NBC, a matsayin wani makamin tsangwamar kafafen watsa labarai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Kamata yayi Lai Mohammed, yana martaba kafafen watsa labarai kamar yadda aikin sa na minista ya ƙunsa, irin yadda ake yi a ƙasashen da suka cigaba a faɗin duniya, amma sai ya koma yana farautar su."

Shugaban na ƴan ƙabilar Ijaw, ya yi Allah wadai da zargin da ministan ya yi wa Peter Obi kan kafa gwamnatin wucin gadi, inda ya ƙyale wasu ƴan Najeriya da suka yi magana akai duk kuwa da cewa, Peter Obi, bai taɓa magana akan hakan ba.

A cewarsa:

"Gaskiya, ni a wajena abin kunya ne ganin abinda Lai Mohammed yake yi da ofishin sa."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Dakatar da Ministan Buhari Kan Abu 1? Gaskiya Ta Bayyana

“Ziyarar sa ta kwanan nan zuwa Amurka kan gwamnatin wucin gadi, domin lalata ƙimar Peter Obi, ni a wajena baya da wani amfani, saboda Lai Mohammed bai kawo wani rahoto daga wata hukuma ba wacce ta tabbatar da zargin da yake yi, amma sai farfaganda kawai domin lalata ƙimar wanda bai ji ba bai gani ba."

An Yi Karar Shugaba Buhari da NBC a Kotu

A wani labarin na daban kuma, wasu ƙungiyoyi biyu sun maka shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da hukumar NBC gaban kotu.

Ƙungiyoyin biyu sun je kotun ne bayan hukumar NBC ta ci tarar wani gidan talbijin a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng