Dubu Ta Cika: An Kama Fursunan daYa Gudu da Gidan Yarin Kuje a Nasarawa

Dubu Ta Cika: An Kama Fursunan daYa Gudu da Gidan Yarin Kuje a Nasarawa

  • Yan sanda sun damƙe ɗaya daga cikin fursunonin da suka tsere daga gidan Yarin Kuje, a jihar Nasarawa
  • Kakakin yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya ce sun cafke Salisu Buhari da abokinsa bisa zargin satar Babura
  • Tuni dai kwamishinan yan sandan Nasarawa ya ba da umarnin miƙa lamarin hannun sashin binciken aikata manyan Laifuka

Nasarawa - Rundunar 'yan sanda reshen jihar Nasarawa ta kama Salisu Buhari, ɗaya daga cikin fursunonin gidan gyaran halin Kuje, wanda ya gudu daga wurin lokacin fashin magarkama a watan Yuli, 2022.

Premium Times ta ce wannan nasara na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Ramhan Nansel, ya fitar ranar Lahadi a Lafia, babban birnin jihar.

Gidan yarin Kuje.
Dubu Ta Cika: An Kama Fursunan daYa Gudu da Gidan Yarin Kuje a Nasarawa Hoto: premiumtimes
Asali: UGC

Nansel, mataimakin Sufuritandan 'yan sanda (DSP) ya ce jami'an sun cafke Buhari tare da abokinsa, Zubairu Ali, bisa zargin satar Babura a yankin ƙaramar hukumar Nasarawa.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Kasurgumin fursunan da ya tsere a magarkamar Kuje ya sake shiga hannu

"Ranar 6 ga watan Afrilu, da misalin ƙare 11 na dare, jami'an 'yan sanda na Caji Ofis ɗin Nasarawa suka cafke wanda ya gudu daga hannu da wani mutum ɗaya bisa zargin Satar Babura."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Rahoton bincuken farko da aka tattara ya nuna cewa mutanen biyu na da hannu a mafi yawan sace-sacen Babura a karamar hukumar Nasarawa da kewayenta."
A cikin Bincike Salisu Buhari ya yi bayanin cewa ya gudo ne daga gidan yarin Kuje lokacin da aka kai hari a shekarar da ta gabata, 2022. Bayan haka ne ya haɗe da abokinsa suka ci gaba da aikata laifuka."

- DSP Ramhan Nansel.

Ya ƙara da cewa kwamishinan 'yan sanda, Maiyaki Muhammed-Baba, ya umarci a miƙa Kes din ga sashin binciken manyan laifuka da ke Lafiya, domin zurfafa bincike.

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta rahoto cewa a ranar 9 ga watan Yuli, 2022, hukumar yan sandan Nasarawa ta kama wani Fursuna da ya gudo, Hassan Hassan.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamna El-Rufai Ya Cire Dokar Kullen Da Ya Ƙaƙaba a Wani Yankin Kaduna

Rundunar Yan Sanda Ta Haramta Al'adar Tashe a Jihar Kano

A wani labarin kuma Rundunar yan sanda ta dakatar da al'adar Tashe a faɗin jihar Kano saboda muhimmin dalili

A wata sanawa, mai magana da yawun hukumar yan sandan Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce sun hana tashe ne saboda yanayin tsaro.

Ya ce gurbatattun mutane na saje wa da masu tashe au aikata muggam laifuka kamar ayyukan yan daba, fashi da makami, kwacen waya ɗa sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262