'Yan Bindiga Sun Yi Amai Sun Lashe, Sun Zaftare Kudin Fansan Da Suke Nema a Zamfara

'Yan Bindiga Sun Yi Amai Sun Lashe, Sun Zaftare Kudin Fansan Da Suke Nema a Zamfara

  • Ƴan bindigan da suka sace mutum 85 a jihar Zamfara sun sassauta kan kuɗin fansan da suka nemi a ba su
  • Ƴan bindigan sun ce yanzu kowane mutum ɗaya dole ne a biya masa N20,000 kafin ya shaki iskar ƴanci
  • Sai dai sun kuma gindaya wasu sharuɗɗan waɗanda dole sai an cika su kafin su sako mutanen da suka sace

Jihar Zamfara- Ƴan bindigan da suka sace mutum 85 a ƙauyen Wanzamai, cikin ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara sun amince su karɓi N20,000 a matsayin kuɗin fansa kan kowane mutum ɗaya da suka sace.

Ƴan bindigan sun kuma nemi hukumomi da su janye sojojin da aka kai zuwa cikin ƙauyen a cikin sharuɗɗan da suka gindiya domin sakin mutanen da suka sace, cewar rahoton Punch

Matawalle
'Yan Bindiga Sun Yi Amai Sun Lashe, Sun Zaftare Kudin Fansan Da Suke Nema a Zamfara Hoto: Punch
Asali: UGC

Jaridar Daily Post ta rahoto cewa a ranar Alhamis da ta gabata, ƴan bindigan suka sace kusan kimanin mutum 100 yankin.

Kara karanta wannan

Ashsha: Yadda Aka Babbake Wani Matashi Kan Zargin Satar Wayar Android, Ya Kone Kurmus

Sun bayyana sharuɗɗan su

Sun bayar da wa'adin ƙarfe 12:00 na daren ranar Lahadi, inda suka yi barazanar halaka duk wani wanda ba a biya masa kuɗin fansarsa ba kafin cikar wa'adin da suka bada.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sun kuma yi barazanar cewa idan dai har ba a janye jami'an sojojin da aka jibge a ƙauyen Wanzamai ba, za su cigaba da sace mutanen ƙauyen.

Wani mazaunin ƙauyen, Abubakar Na'Allah ya gayawa majiyar mu ta wayar tarho cewa ƴan bindiga sun turo saƙo cewa N20,000 kawai za su ƙarba kan kowane mutum ɗaya da suka sace a matsayin kuɗin fansa, duba da cewa talakawa ne marasa ƙarfi.

A cewarsa:

“Da farko ƴan bindigan sun nemi da a basu N50m domin sakin mutum 85 ɗin da suka sace waɗanda mafi yawa daga cikinsu mata ne da ƙananan yara da suka shiga daji samo makamashi a ranar Juma'ar da ta wuce.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Yan Bindiga Sun Sace Matasa Sama da 80 Yau Jumu'a a Jihar Arewa

“Amma bayan kwashe dogon lokaci ana tattaunawa, sun amince su karɓi N20,000 daga kowane mutum ɗaya da suka sace saboda sun fahimci cewa dukkaninsu talakawa ne."

Na'Allah ya bayyana cewa iyalan waɗanda aka sacen suna ta ƙoƙarin biyan kuɗin inda ya koka kan cewa da yawa daga cikin su, suna ta siyar da ɗan abinda suka mallaka domin haɗa kuɗin.

Yan Bindiga Sun Kashe ASP Tare da Raunata Wasu Jami’ai a Shingen Bincike

A wani labarin na daban kuma, 'yan bindiga sun farmaki jami'an tsaro sun halaka ɗaya daga ciki, yayin da wasu da dama suka samu raunika.

Lamarin dai ya auku ne yayin da jami'an tsaron ke bakin aikin su a shingen bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng