Kungiyar NUSAID Ta Gwangwaje Mutum 750 da Kayan Abinci a Birnin Kano

Kungiyar NUSAID Ta Gwangwaje Mutum 750 da Kayan Abinci a Birnin Kano

  • Wata kungiya a jihar Kano ya gwangwaje mazauna da kayayyakin abinci domin rage radadin talauci a watan Ramadana
  • Akalla mutum 750 ne suka samu wannan tallafin da aka raba a ranar Lahadi 9 Afirilu, 2023 a birnin na Kano
  • Watan Ramadana na daya daga cikin watannin da Musulmai ke yawan bukatuwa da abinci kasancewar suna azumi

Jihar Kano - Masu karamin karfi 750 a jihar Kano sun samu tallafin kayan abinci a cikin watan Ramadana daga wata kungiya mai zaman kanta.

Kungiyar mai suna NUSAID ta yi wannan aikin ne a ranar Lahadi 9 Afirilu, 2023 tare da hadin gwiwar zauren hadin kan malaman jihar Kano, Aminiya ta ruwaito.

A cewar rahoto, kungiyar dama ta saba irin wannan rabo, wanda a bana ya hada marayu, mata da sauran masu karamin karfia cikin watan mai alfarma.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Yadda dan kasar waje ya shigo Najeriya da kayan hodar iblis a cikin kwaroron roba

An yi rabon abinci a Kano
Yadda aka raba kayan abinci ga mabukata a Kano | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Yadda aka yi rabon a jihar Kano

Da yake bayani kan dalilin raba wadannan kayayyakin, Dr Sa’idu Ahmad Dukawa, mai kula da shirin ya ce, sun yi hakan ne don rage radadin talauci ga masu azumi a jihar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa:

“Mutum 750 ne suka samu wannan tallafin na yau, kuma abin da ke ciki kayan abinci ne sai ’yan kudin mota.
“A cikin kowanne kunshi akwai shinkafa da taliya da kafi-zabo da man gyada da dabino da sukari da kuma gishiri.”

Meye manufar kungiyar na wannan rabon?

Da yake bayyana manufar kungiyar na tallafawa masu karamin karfi, Dr. Dukawa ya ce:

“Babbar manufarmu ta yin wannan aikin alherin ita ce ta rage wa masu azumi radadin halin da suke ciki, musamman a wannan watan na azumi.”

A bangaren wadanda suka ci gajiyar shirin, sun bayyana jin dadi da yabo ga kungiyar tare da yin addu’o’in alheri bisa samun wannan alheri.

Kara karanta wannan

Wani mummunan abu ya faru: An kame kasurguman 'yan 'Sara-Suka' a jihar Bauchi

Ya halasta miji ya sadu da matarsa a watan Ramadana

A wani labarin kuma, wani malamin addinin Islama ya yi fadakarwa ga al’ummar Musulmi game da watan azumin Ramadana.

Malamin ya ce, halal ne ga Musulmi ya sadu da iyalinsa a cikin watan Ramadana, amma a wani kebabben lokaci.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da wasu ke yawan tambayoyi game da hukunce-hukuncen azumin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.