Jami’an ’Yan Sanda Sun Kama Kasurguman ’Yan Daba 7 a Jihar Bauchi
- An kama ‘yan Sara Suka a jihar Bauchi bayan samun bayanan sirri game da barnar da suke aikatawa a wani yankin jihar
- Bincike ya kai ga cewa, an gano suna dauke da muggan makamai da kuma kayayyakin bugarwa masu sanya maye a tare dasu
- Ya zuwa yanzu, kwamishinan ‘yan sanda ya ce za a gurfanar dasu bayan kammala binciken da ya dace kamar yadda doka ta tanada
Jihar Bauchi - Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kame wasu mutum bakwai da ake zargin ‘yan daba ne daga wata maboyarsu da ke unguwar Magaji.
Wannan na fitowa ne daga cikin wata sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ahmad Mohammed Wakil ya fitar, rahoton Channels Tv.
A cewar sanarwar, wadanda aka kaman sun hada da Rayyanu Mohammed, Mustapha Harisu, Yusuf Ibrahim, Mubarak Lawal, Abubakar Musa, Al-Amin Hussaini da Hamza Umar.
Ta kuma kara da cewa, gaba dayan matasan sun kasance ‘yan tsakanin shekaru 17 ne zuwa 25 kuma an kama su dauke da makamai masu illa da kayan maye.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
‘Yan Sara Suka aka kama, inji ‘yan sanda
Kama sun, inji ‘yan sanda ya zo ne bayan samun bayanan sirri daga hukumomin tsaron jihar bisa irin barnar da suke aikatawa, rahoton Tribune Online.
A cewar kakakin na ‘yan sanda, a halin da ake ciki ana ci gaba da binciken kan wadanda ake zargin da kuma wadanda suke tare dasu a boye.
Hakazalika, ya ce bincike ya gano cewa, wadanda aka kaman ‘yan daban haramtacciyar kungiyar ‘yan daban da ke addabar mutanen Bauchi ne; Sara Suka.
Za a gurfanar dasu a gaban kotu
Da yake martani game da kamun, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Aminu Alhassan ya yi kira ga iyaye da su kula da tarbiyyar ‘ya’yansu tare da daura su kan turba mai kyau.
Ya kara da cewa, dukkan wadanda aka kaman za a gurfanar dasu a gaban kotu don yi musu hukunci daidai da barnar da suka aikata kamar yadda doka ta tanada.
An kama fursunan da ya tsere a Kuje
A wani labarin kuma, kun ji yadda aka kama wani matashin da ya tsere daga magarkamar Kuje da ke babban birnin tarayya Abuja.
Wannan na zuwa ne bayan da ya sake aikata laifi a wani yankin jihar Nasarawa tare da wani abokin cin mushensa.
Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da bincike kafin daga bisani a dauki matakin doka da ya dace game da laifin da ya aikata.
Asali: Legit.ng