An Kama Wani Matashin da Ya Tsere Daga Gidan Yarin Kuje a Harin ’Yan ISWAP
- ‘Yan sanda sun kame wani matashi da ake zargin ya tsere daga gidan yarin Kuje da aka farmaka a shekarar da ta gabata
- An kuma kama shi tare da wani mutum da ake zargin sun yi kwacen babur a wani yankin jihar da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya
- Ba wannan ne karon farko da ake kama wadanda suka tsere daga gidan yarin da aka farmaka a shekarar da ta gabaa ba
Jihar Nasarawa - Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta yi nasarar kame wani fursunan da ya tsere da gidan yarin Kuje a harin ‘yan ta’adda na shekarar da gabata a Abuja, Daily Post ta tattaro.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ramhan Nansel ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, inda ya bayyana cewa, wanda aka kamen matashi ne mai shekaru 24 mai suna Salisu Buhari dan asalin jihar Nasarawa.
Hakazalika, an kama wani tare da Salisu a wani aikin ‘yan sanda a karamar hukumar Nasarawa ta jihar mai suna Zubairu Ali mai shekaru 27.
Meye laifin da suka aikata?
Dukkansu biyun an kama su ne a ranar Alhamis din da ta gabata bisa zarginsu da sace babur, kamar yadda rahoton Channels Tv ya bayyana.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar sanarwar:
“Binciken farko ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun yi kwancen babur tare da sace shi a karamar hukumar Nasarawa da kewayenta.
“Bayan titsiye su, Salisu Buhari ya amsa laifinsa na tserewa daga magarkamar Kuje a lokacin da aka farmaki gidan yarin a bara, inda ya hade da abokinsa, kuma suka ci gaba da aikata barnarsu.”
DSP Nansel ya ce, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Maiyaki Baba ya umarci a mayar da kundin matasan biyu zuwa sashen binciken manyan laifuka da ke Lafia don yin cikakken bincike.
Fursunoni sama da 300 ne suka tsere a harin gidan yarin Kuje
A tun farko, kunji yadda rahotanni suka bayyana adadin wadanda suka tsere a lokacin da ‘yan ta’adda suka kai farmaki a gidan yarin Kuje.
A cewar rahotannin tsaro, akalla fursunoni 300 ne suka fece daga gidan yarin na Kuje da ke babban birnin tarayya Abuja.
Idan baku manta ba, a ranar Talata 5 ga watan Yulin 2022 ne wasu ‘yan ta’adda suka kai mummunan farmaki kan gidan yarin.
Asali: Legit.ng