Shekaru Bayan Yi Mata Sata, Matashi Ya Dawo Ga Mata Mai Shago, Ya Ba Ta Kyautar N100k

Shekaru Bayan Yi Mata Sata, Matashi Ya Dawo Ga Mata Mai Shago, Ya Ba Ta Kyautar N100k

  • Wani dan Najeriya ya jika zukatan al’umma yayin da ya dawo wurin matar da ya taba yi mata sata shekarun da su wuce
  • Ya ziyarci shagonta, inda ya sayi kayayyaki kafin daga bisani ya bayyana mata laifin da ya taba aikata mata a baya
  • Kamar ba komai ba, haka ya dauki wasu adadin kudade masu yawa ya damka mata tare da gode mata

Wani dan Najeriya ya jika zuciyar wata mata yayin da ya gwangwaje ta da kyautar N100,000 a madadin mayar mata da kayan da ya sace mata a shekarun baya.

Mutumin mai suna Theo Ayomoh ya ziyarci shagon matar, inda ya sayi biskit tare da cewa, a nan ya taba satar alawa.

Daga nan, ya gabar da kansa, inda yace a lokacin yana yaro ta taba kama shi lokacin da ya yi mata satan alawa, bai wuce shekaru takwas ba.

Kara karanta wannan

Biyu Babu: Wani Ya Damfari Yar Gidan Magajiya A Abuja, Bai Biya Ta Kudin Aiki Ba Kuma Ya Sace Wayarta

Ya kuma bayyana cewa, ba wancan karon bane na farko da ya yi mata sata, kawai dai ta yi nasarar kame shi ne a wancan ranan.

Matashi ya yiwa matar da ya yiwa sata kyautar kudi
Lokacin da matashin ya zo shagon matar | Hoto: @theoayoms
Asali: TikTok

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Theo ya nuna godiya da kuma yaba mata bisa koya masa hali mai kyau na hana shi sata da kuma kin fada wa iyayensa. Musamman ya durkusa a kasa don gode mata.

Wannan ya faru ne bayan da ya dauko kudi N100,000 ya ba ta tare da kalaman godiya. Matar ta shiga mamaki da ganin wannan rana.

Kalli bidiyon:

Jama’ar kafar sada zumunta sun yi martani

Yayin daka yada bidiyon, jama’a a kafar sada zumunta sun yi martani mai daukar hankali game da wannan lamarin da ya faru. Ga kadan daga abin da mutane ke cewa:

@monicaihezuoh:

"Rayuwar yarinta..muna sata har na iyayenmu ma, bansan meye yake sa muke yin haka ba.”

Kara karanta wannan

"Kan 300k": Yadda Uba Ya Gwada 'Yarsa Don Ya Gane Ko Tana Taba Sana'ar Karuwanci a Makaranta

@Faith Macauley:

"Ina sonka Allah ya yi maka albarka, don Allah ina son zama abokinka.”

@Ogefoodies:

"Allah ya maka albarka da ka gane gaskiya.”

@Dondaddy007:

"Dan uwa Allah zai albarka ce ka dalilin wannan. Zuciya mai tsafta.”

@Hyajide:

"Ka saka ni hawaye dan uwa, Allah ya yi maka albarka kuma muna godiya mama.”

@user9754544349547:

"Ka yi kokari sosai, Theo.... Allah ya ci gaba da dafa maka a kokarin rayuwarka.”

@user6806211506724:

"Mai da alheri na da kya. Ya yi kyau, tunaninka na da kyau, misali nagari, Allah ya yi maka albarka.”

Wata dattijuwa kuwa na neman taimako bayan da ta rasa mai ba ta aiki a sana'ar da take na daben tayel.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.