‘Ina Neman Taimako’: Wata Mata Mai Shekaru 58 da Ke Sana’ar Dabe Tana Neman Taimakon Jama’a

‘Ina Neman Taimako’: Wata Mata Mai Shekaru 58 da Ke Sana’ar Dabe Tana Neman Taimakon Jama’a

  • Wata mata mai shekaru 58 ‘yar jihar Bayelsa, Rose Nwokocha na neman taimakon yadda za ta fita daga wani yanayi
  • A cewar matar, duk da cewa ta kware a sana’ar daben tayel, mutane basu son ba ta aiki saboda ta tsufa
  • Tana neman madadin wannan sana’ar, inda tace da za ta samu jari, za ta fara siyar da iskar gas na girki

Labarin wata mata mai shekaru 58 ‘yar jihar Bayelsa, Rose Nwokocha ya yada a kafar sada zumunta a lokacin da wani @KingErefitei ya yada hotunanta a kafar sada zumunta.

Rose dai na sana’ar daben daki na tayel ne domin iya rike ‘ya’yanta hudu. Duk da kwarewarta a sana’ar, ta ce tana fuskantar matsala wajen samun kwastomomi domin kuwa ta tsufa.

A wata tattaunawa da wakilinmu Joseph Omotayo, matar ta ce ta iya sana’o’i daban-daban masu daukar hankali.

Kara karanta wannan

LP: Yadda Aka Shiryawa Peter Obi Tarkon ‘Yan Mata da Kudi Domin Ganin Bayan Shi

Hotunan mata mai shekaru 58 da ke daben tayel sun ba da ammaki
Yadda mata mai shekaru 58 ke yin tayel | Horo: @ndinsider
Asali: Twitter

A cewar Rose, ta iya aikin gini, za ta iya fara gini daga tushe har zuwa karshensa ba tare da wata matsala ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matar, wacce da fari aka yada labarinta a Nigeri Delta Insider, ta ce bata samu haihuwa da wuri ba, don haka ‘ya’yanta guda hudu gaba daya sun dogara ne da ita.

Rose mace ce mai kokarin gaske

A cewarta, bata jin kunyar yin aiki tukuru domin neman halaliyarta na kudi don kula da kuma magance matsalolinta.

Duba da shekarunta, an tambaye ta meye za a iya yi mata don ganin an taimaka mata, sai tace:

“Ina son mallakar shagon gas inda mutane za su ke saye a kilo-jilo. Zan so idan mutane za su taimake ni na cimma wannan burin.”

Mai so ya taimaki Rose, ga lambar waya: 08063740364.

Martanin jama’a a kafar sada zumunta

Kara karanta wannan

Rai Bakon Duniya: Matar Gwamnan Kano Na Farko, Ladi Bako, Ta Rasu Tana Da Shekaru 93

Bayan yada hoton a Twitter, Legit.ng ta tattaro muku kadan daga martanin jama’a da kuma abin da suke cewa kamar haka:

ObiomasHandbag:

"Na ga matar jiya a wani yankin aikinmu inda take ba da labarin yadda a yadu ga wata mai kawo mana kaya wacce ta kasance matar fastonta kuma kawarta.”

@gallaries55:

"Abin burgewan shine lafiyarta kalau. Mutane nawa ne za su iya sunkuyo don irin wannan aikin? Allah ya taimake ta ta inda bata tsammani.”

Ontymgirl:

"Wow. Tana kokari fa. A 2018 sana’ar tayel nake yi har sai da na samu wani babban aikin dabe tare da mai gida na da abokan aiki ba, bayan daukar 60x60 na tayel zuwa saman bene bana iya tsayuwa da kyau ko tafiya da kyau. Dole na bar aikin don jinyar kaina.”

@Baianoanfield:

"Sarauniya na yi mai yiwuwa domin ganin ta tsira da kuma horar da ‘ya’yanta... Jinjina.”

Kara karanta wannan

"Ko Ba Shi Da Hannu Zan Zauna Da Shi": Labarin Zazzafar Son Da Jaruma Rakiya Moussa Ke Yi Wa Wani Mawaki Ya Girgiza Intanet

Wani bidiyo kuma, ya nuna lokacin da dalibai ke yiwa motar wani lakcara isgili bayan shigowarsa cikin makaranta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.