Yan Bindiga Makiyaya Sun Kai Sabon Mummunan Hari Kan Yan Gudun Hijira a Benue

Yan Bindiga Makiyaya Sun Kai Sabon Mummunan Hari Kan Yan Gudun Hijira a Benue

  • Ana fargabar akalla mutane 43 suka rasa rayukansu a wani sabon harin yan ta'addan makiyaya a jihar Benuwai
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun aikata wannan ɗanyen aikin ne da misalin karfe 10:00 na daren jiya Jumu'a
  • Hukumar yan sanda reshen jihar Benuwai ta tabbatar da faruwar lamarin amma ta ce zata tattara bayanai cikakku tukuna

Benue - Aƙalla 'yan gudun Hijira 43 ake fargabar sun rasa rayukansu a wani sabon harin da Fulani makiyaya suka kai makarantar Firamare da ke Mgban, ƙaramar hukumar Guma, jihar Benuwai.

Duk da babu cikakken bayani kan lamarin amma jaridar Vanguard ta tattaro cewa makarantar Firamaren na cikin wuraren da aka tsugunar da 'yan gudun hijira.

Taswirar jihar a Benuwai.
Yan Bindiga Makiyaya Sun Kai Sabon Mummunan Hari Kan Yan Gudun Hijira a Benue Hoto: punchng
Asali: Twitter

Haka zalika bayanai sun nuna cewa 'yan ta'addan fulani makiyayan sun kai farmaki kan mutanen da ke zaune a sansanin da misalin karfe 10:00 na daren ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Bauchi Ta Ɗage Zaman Muƙabala Da Sheikh Dr Idris Abdulaziz

Wata majiya ta bayyana cewa daga cikin gawar mutane 43 da kawo yanzun aka gano har da Mata masu juna biyu da kuma kananan yara, yayin da wasu da yawa suka samu raunuka.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban ƙaramar hukumar Guma, Mike Aba, wanda ya yi magana ta bakin wani jami'in tsaron ƙaramar hukumarsa, Christopher Waku, ya bayyana harin da kisan ƙare dangi.

Mista Waku, wanda ya shaida wa Punch cewa yana magana ne daga wurin da lamarin ya faru, ya bayyana cewa sun ɗauko gawarwakin mutane 24 a cikin Azuzuwan da mutane ke zaman gudun hijira.

Ya kara da cewa bayan waɗan nan sun kuma tsinto gawarwakin wasu mutum 10 a kan Titi, wanda ya nuna sun yi yunƙurin guduwa daga harin amma harsashi ya same su.

Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar yan sanda reshen jihar Benuwai, Catherine Anene, ta tabbatar da kai harin amma ta nemi a ba ta lokaci domin ta haɗa cikakkun bayanai.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Wa Jami'an Tsaro Kwantan Bauna, Sun Kashe Da Dama

Yan ta'adda sun yi garkuwa da matasa 80

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Sace Matasa Maza da Mata Akalla 80 a Jihar Zamfara

Rahotanni sun nuna cewa matasan sun shiga hannun masu garkuwa ne lokacin da suka shiga cikin jeji ɗebo itatuwan girki a kauyen Wanzamai ranar Jumu'a da safe.

Mazauna garin sun ce lamarin ya shafi kowa da kowa kuma har yanzun maharan ba su tuntuɓi kowa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262