Yan Bindiga Sun Sace Mutum 100 Daga Gonakinsu A Zamfara Da Katsina Cikin Watan Ramadan
- Wasu yan bindiga sun sace a kalla mutane 100 daga gonakinsu a jihohin Katsina da Zamfara
- Majiya daga Wanzamai, wani gari da ke iyakar jihar Zamfara da Katsina ta tabbatar da afkuwar lamarin
- Maharan sun kuma kutsa garin Kucheri da Yankara da ke jihar Katsina inda nan ma suka sace mutane
Hankulan mutane sun tashi yayin da yan bindiga suka sace a kalla mutane 100 daga gonakinsu a jihohin Zamfara da Katsina.
Daily Trust ta tattaro cewa maharan dauke da bindigu sun kai hari a Wanzamai, wani gari da ke kan iyakan jihohin Zamfara da Katsina.
A baya, yan bindiga sun sha kai hare-hare a garin da ke kan babban hanyar Gusau zuwa Funtua.
Mazaunin garin ya tabbatar da sace mutane a kalla 100
Wani mazaunin kauyen Wanzamai a karamar hukumar Tsafe na jihar Zamfara wanda ya ce sunansa Sani Wanzamai ya ce a kalla yara 80 aka sace daga kauyen Wanzamai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sannan an sace mutum fiye da 20 daga kauyen Kucheri a karamar hukumar Tsafe na jihar da garin Yankara a jihar Katsina da ke makwabtaka da su.
A cewarsa:
"A yayin da yaran sun tafi daji don nemo itace, sauran manyan an kama su ne a gonakinsu lokacin da suka tafi sharan gona don shirin noman daminan bana. Akwai mata cikin wadanda aka sace din.
"Maharan sun bayyana ba zato ba tsammani suka tisa keyar wadanda suka sace cikin daji. Har yanzu bata garin ba su tuntubi iyalan wadanda suka sace ba. Wasu sun yi kokarin tuntuban yan uwansu amma ba su yi nasara ba."
Martanin yan sanda
An yi kokarin ji ta bakin mai magana da yawun yan sandan jihar CSP Muhammad Shehu amma ba same shi ba a lokacin hada wannan rahoton domin wayarsa na kashe.
Hankula Sun Tashi Yayin Da Mutane Da Dama Suka Yi Batar Dabo Sakamakon Mummunan Hadarin Jirgin Ruwa A Bayelsa
Wasu Yan Ta'adda Masu Fitinar Mutanen Jihar Nasarawa Da Abuja Sun Shiga Hannu
Rahoto ya zo cewa jami'an yan sanda na birnin tarayya Abuja sun yi nasarar kama wasu mambobin wata kungiyar yan fashi da ake zarginsu da aikata laifuka a Nasarawa da Abuja.
Kwamishinan rundunar yan sanda a Abuja, Sadiq Abubakar ya bayyana cewa an kama wadanda ake zargin ne a wani gari mai suna Masaka a jihar Nasarawa da ke kusa da Abuja.
Asali: Legit.ng