Ba Za Mu Yarda Da Shirin Cire Tallafin Man Fetur Da Ake Yi Ba, Matasan Arewa

Ba Za Mu Yarda Da Shirin Cire Tallafin Man Fetur Da Ake Yi Ba, Matasan Arewa

  • Wata kungiyar matasan arewacin Najeriya ta ce ba zata amince da yunkurin cire tallafin man fetur ba
  • Kungiyar ta ce cire tallafin zai kara jefa talaka cikin matsi akan wanda ya ke fama da shi na tsadar rayuwa
  • Kungiyar ta yi kira ga sauran kungiyoyi da su tashi tsaye wajen neman ceto talaka daga abin da ake shirin yi

Jihar Kaduna - Wata kungiya, kungiyar matasan arewacin Najeriya, 'Northern Youth Council of Nigeria', ta gargadi gwamnati tarayya game da yunkurin cire tallafin mai, tana mai cewa ba za a juri haka ba, The Punch ta rahoto.

Yayin nuna adawa da cire tallafin, kungiyar ta bayyana irin matsalar da hakan zai haifar ga yan Najeriya "da dama su ke cikin matsin tattalin arziki."

Tallafin Man Fetur
Kungiyar matasan Arewa ta ce ba ta goyon bayan cire tallafin man fetur. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Abin da yasa muke adawa da cire tallafin mai - Isa Abubakar, Shugaban Northern Youth Council of Nigeria

Kara karanta wannan

An matsa mani lamba: Bayan tono asirinsa, Peter Obi ya fasa kwai game da zaben 2023

Shugaban kungiyar, Alhaji Isa Abubakar, wanda ya bayyana haka a Kaduna ranar Alhamis, ya bayyana tsoron kada wasu tsiraru su yi awon gaba da duk wani tallafi da zai rage radadin cire tallafin, kamar yadda ya faru da tallafin COVID-19.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka nan, kungiyar ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta sake duba batun cire tallafin, ta na cewa hakan zai kara kunci a rayuwar talaka, wanda bukatun yau da kullum ke gagara.

Ta kuma shawarci gwamnati da ta mayar da hankali wajen samar da aikin yi don bunkasa tattalin arziki.

"Ba za mu iya jure sake jefa mutanen Najeriya a wahala ba, musamman matasa da ke fama da tsananin rashin aikin yi da rashin ba su dama," in ji shi

Ya ce akwai hukunci ga duk wanda ke son jefa yan Najeriya wani hali musamman idan bukata ta dawo da shi lokacin siyasa.

Kara karanta wannan

Ahaf: Gwamnatin Buhari ta gano kasashen Turai na daukar nauyin ta'addanci, sun sha suka

"Su tuna yadda aka kayar da wasu gwamnoni a zaben da ya gabata za su fahimci cewa yanzu iko na hannun talakan Najeriya. Yan Najeriya ba za su manta ba.
"Kungiyar matasan ta ce ba za ta amince da duk wani yunkuri na cire tallafin mai ba kuma ta na kira ga sauran kungiyoyi da su tashi su taya yan Najeriya yaki," a cewar shi

Da na zama shugaban kasa zan cire tallafin mai, Peter Obi

Mista Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP ya ce da zarar ya yi nasarar zama shugaban kasa zai cire tallafin mai.

Obi ya ce tallafin shiryayyen ta'addanci ne da wasu tsiraru ke amfana da shi a kasar, kuma zai karo karshen hakan da zarar ya hau kan mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164