Likitocin Najeriya sun bar mutane a Karkara sun tare a Abuja da Legas, Ministan Kwadago

Likitocin Najeriya sun bar mutane a Karkara sun tare a Abuja da Legas, Ministan Kwadago

  • Ministan Kwadago ya ce Likitocin Najeriya sun tare a birane shiyasa ake ganin babu Likitoci
  • Ngige ya yi tsokaci ne kan yadda Likitoci ke guduwa daga Najeriya
  • Wata daya kenan da Likitocin Najeriya suka shiga yajin aiki

Abuja - Ministan Kwadagon Najeriya, Chris Ngige, yace Najeriya na da isassun Likitoci amma yawancinsu sun gudu aiki birnin tarayya Abuja, Legas da garin Fatakwal.

Ngige ya bayyana hakan ne a taron kwamishanonin lafiyan jihohin Najeriya a ranar Juma'a, 3 ga Satumba, 2021.

Kamfanin dillancin Labarai NAN ta ruwaito cewa an shirya taron ne don tattauna yadda za;a inganta kiwon lafiya a Najeriya.

Ngige yace Najeriya Najeriya ba zata iya cika sharadin majalisar dinkin duniya ba na yawan Likitocin da ya kamata ace kasa na da shi.

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisa sun fadi ainihin dalilin tsige su Nanono, sun ce ba don Allah aka yi ba

Yace:

"Mu ba kasar majalisar dinkin duniya bane, mu kasa ce mai cigaba. Saboda haka zamuyi amfani da abin da muke dashi."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Likitoci nawa muke da shi a karkara tun da kowa ya gudu birni. Kusan kowa ya dawo Abuja, Legas da Fatakwal da zama. Kuma muna da asibitoci 10,000 kuma babu Likitoci."

Likitocin Najeriya sun bar mutane a Karkara sun tare a Abuja da Legas, Ministan Kwadago
Likitocin Najeriya sun bar mutane a Karkara sun tare a Abuja da Legas, Ministan Kwadago Hoto: Doctors
Asali: Twitter

Duk laifin gwamnonin Najeriya ne

A taron, Kwamishanan Lafiya jihar Legas, Abayomi Akin, ya yi kira ga gwamnonin Najeriya su inganta lamarin lafiya ga Likitoci a jihohinsu.

Abayomi yace akwai Likitocin Najeriya sama da 20,000 dake aiki a kasar waje yanzu.

Yace:

"Shiyasa nike kira ga gwamnoni sun inganta abubuwa don Likitoci. Yanzu ba maganar guduwar Likitoci kasashen waje ya kamata mu rika magana kai ba, kamata yayi muyi magana kan dawo da su."

Kara karanta wannan

Talauci: Rahoto ya nuna 'yan Najeriya miliyan 27 ke samun kudin shiga N100k a shekara

Likitoci a Najeriya sun tsunduma yajin aiki ranar Litinin

Kungiyar likitoci a kasar nan (NARD) ta umurci mambobinta dasu tsunduma yajin aikin sai baba ta gani ranar Litinin, 2 ga watan Agusta.

Da yake yiwa yan jarida bayani a karshen taron, Shugaban kungiyar, Dr Okhuaihesuyi Uyilawa ya bayyana cewa an umurci mambobin dasu fara yajin aikin sai baba ta gani.

Mutane na kwashe yan uwansu daga asibiti

Yan uwa na kwashe marasa lafiyansu daga asibitocin gwamnati yayinda yajin aikin kungiyar Likitoci masu neman kwarewa (NARD) ya shiga kwana ta biyu.

Jaridar Sun ta bayyana cewa a asibitocin da ta ziyarta, Likitoci sun dauke kafa gaba daya kuma an bar marasa lafiya babu mai duba su.

Hakazalika an fadawa wadanda suka kawo sabbin marasa lafiyansu su tafi asibitoci masu zaman kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel