Ayyuka 14 da Buhari Ya Yi wa Kudu da Babu Shugaban da Ya Kama Kafarsa a Tarihi
- Duk da suka da musamman ‘yan adawa su ke yi wa shugaba Muhammadu Buhari, gwamnatinsa tayi zarra a wasu wurare a shekaru 8
- Masu nazari su na cewa daga cikin inda gwamnatin Muhammadu Buhari tayi fice akwai gina abubuwan more rayuwa domin al’umma
- Tolu Ogunlesi yana cikin masu ba shugaban Najeriya shawara, ya na kokari wajen wanke gwamnatin mai gidansa daga masu suka
Abuja - Da yake fayyace zare da abawa kamar yadda ya saba a shafin Twitter, Tolu Ogunlesi ya jero wasu daga cikin alheran gwamnatin nan.
Mista Ogunlesi ya fado irin ayyukan da Buhari ya yi wa jihohin Kudu, ganin har gobe ana sukarsa a yankin da cewa bai tsinana masu komai ba.
Daga lokacin da Muhammadu Buhari ya zama shugaban kasa zuwa yau, an samu:
1. Katuwar sabuwar tashar ruwa da aka gina a Legas.
2. Sababbin tashoshin kan tudu da aka soma kuma aka karasa
3. Mallaka tashar ruwan Onitsha kuma ya fara aiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Baya ga haka akwai:
4. Sabon sansanin sojojin ruwa a Imo.
5. Sabon sansanin sojojin sama a Enugu.
6. Sasanta rikicin kamfanonin raba wuta na Enugu da sauran ayyukan TCN.
7. Kammala gidan tarihin tunawa da Zik bayan shekaru 20.
Hadimin yake cewa kafin zuwan Buhari, babu wata tashar kan tudu da ake da ita a duk Najeriya.
Yanzu maganar da ake yi, akwai manyan tashoshin kan tudu bakwai wanda ake iya sauke kaya a kasar nan, dukkansu su na karkashin ‘yan kasuwa ne.
A cewar Mai ba shugaban na Najeriya shawara, tun 1999 zuwa yau, babu wani shugaban da ya yi wa Kudu maso gabashin Najeriya kokarin irin uban gidansa.
Daga ciki akwai:
1. Naira biliyan 2 ta karkashin tsarin Sukuk domin gina hanyoyin yankin.
2. Aikin hanyar Enugu zuwa Onitsha.
3. Doka da aka kawo da ta ware $10m domin ‘yan kasuwa su gina matatu.
4. Hanyar tashin jirgin kasa da aka yi a Enugu
5. Dala miliyan 5 da aka ware domin binciken lafiya a Umuahia.
6. Biyan fansho ga 'yan sandan Biyafar bayan shekaru 20.
7. Gadar Neja
Zargin sata a hukumar NIMASA
Tsawon shekaru ana shari’a tsakanin Gwamnatin tarayya da Patrick Akpobolokemi a kotu, an ji labari lauyoyin EFCC sun samu yadda su ke so a zaman karshe.
Ana tuhumar Dr. Patrick Akpobolokemi da satar N725m da samun filin a Banana Island lokacin da ya samu mukami, kotu ta ce gwamnati ta fara rike dukiyoyin.
Asali: Legit.ng