Asirin Dan Sandan Bogi Da Abokinsa Ya Tonu, Sun Fada Komar Yan Sandan Ainihi

Asirin Dan Sandan Bogi Da Abokinsa Ya Tonu, Sun Fada Komar Yan Sandan Ainihi

  • Yan sanda a Jihar Ekiti sun kama mutum biyu da ake zargi da fashi bayan shigowarsu jihar daga Jihar Delta
  • Hukumar ta ce daya daga ciki na yin sojan gona a matsayin dan sanda, kuma ta kama mota da ake zargi satowa su ka yi daga Jihar Delta
  • Rundunar yan sanda ta yabawa kokarin al'umma bisa ba su bayanai akan lokaci don daukar matakin da ya dace

Jihar Ekiti - Jami'an yan sanda a Jihar Ekiti sun kama mutum biyu da suka shigo daga Jihar Delta bisa zargin fashi, The Punch ta rahoto.

Kwamishinan yan sanda, Dare Ogundare, ya ce sashen kula da satar ababen hawa na hukumar ya kamo karamar motar bas, wadda ake zargin su biyun sun sato daga Jihar Delta.

Wadanda ake zargi
Dan sandan bogi da abokinsa da aka kama kan fashi a Ekiti. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Karin Bayani: A Watan Azumi, 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Sarki Mai Martaba a Arewa

Kwamishinan, a wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar, Sunday Abutu, ya fitar mai taken "Rundunar yan sandan Ekiti ta kama mutane biyu bisa zargin fashi, sun gano motar da aka sace", ya ce an kama su biyun, Asimiyu da Oyewunmi, a Ado Ekiti bayan samun rahoto.

Ya ce:

"Bincike ya nuna cewa daya daga cikin wanda ake zargi, Asimiyu, na da kakin sanda da takardun aiki da ya ke sojan gona a matsayin dan sanda a Jihar Delta."

Kwamishinan ya ce:

"Sashen kula da satar ababen hawa na rundunar yan sandan Ekiti, ranar 31, ga watan Maris, 2023, sun samu bayanai game da yan fashin cewa an gano su a Agric-Olope da ke Ado Ekiti a karamar motar Suzuki da aka fi sani da Akoto.
"Da samun bayanan, jami'an sun shiga aiki, sun isa yankin tare da kama mutum biyun.
"Bayan bincike, an gano cewa sun fito ne daga Jihar Delta, inda su ke gudanar da fashin.

Kara karanta wannan

Matasa Sun Zane Wani Basaraken Arewa Dukan Kawo Wuka, Sun Kona Fadarsa

"Sun zo Ekiti da nufin cigaba da aikata laifin. Kuma motar da aka kama rahotanni sun bayyana cewa yan sandan Jihar Delta sun ce sace ta aka yi."

Kwamishinan, ya ce za a mayar da wanda ake zargi ga yan sandan Jihar Delta don fadada bincike, ya kuma yabawa kokarin al'umma wajen bayar da bayani lokacin da ya dace don gudanar da kamen.

Ogundare, ya kuma bukaci mazauna Ekiti "su cigaba da sanya ido akan duk wani mutum ko tawaga da su ke zargi su kuma kai rahoton gaggawa ga ofishin yan sanda mafi kusa don daukar mataki."

An damke wasu matasa uku kan laifin sace yarinya a Kano

A bangare guda yan sandan jihar Katsina sun kama wasu matasa uku kan zarginsu da sace wata yarinya yar shekara shida.

Mai magana a yawun rundunar yan sandan Kano, Gambo Isah, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya ce matasan uku sun hada baki ne wurin sace yarinyar a unguwar Bachirawa a Kano a watan Janairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164