Kudu Maso Gabas Ya Kamata a Ba Shugabancin Majalisar Dattawa, Inji Kungiyar Matasan Arewa
- Kungiyar matasa ‘yan Arewa sun bayyana yankunan da ya kamata a ba shugabancin majalisun kasar nan guda biyu
- Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ake ci gaba da ganin masu bayyana sha’awar hawa kujerun guda biyu masu daraja
- A baya, Abdulaziz Yari ya bayyana bukatar a ba shi ikon zama shugaban majalisar dattawa a Najeriya
Jihar Kaduna - Gabanin rantsar da majalisar tarayya ta 10 a watan Yunin 2023, wata kungiyar ‘yan Arewa ta ba da shawari ga shugabannin ACP kan shugabancin majalisa.
Kungiyar Arewa Young Professional in Politics ta bukaci jam’iyyar APC ta tabbatar da cewa ta ba yankin Kudu maso Gabas shugabancin majalisar dattawa.
A cewar kungiyar, yin hakan ne zai nuna adalci, daidaito da kuma damawa da ‘yan yankin a shugabancin kasar, Channels Tv ta ruwaito.
A wani taron manema labarai a Kaduna, kungiyar ta bayyana cewa, ba yankin Kudu maso Gabas shugabancin majalisar dattawa zai yiwu ne ba tare da la’akari da sakamakon zaben shugaban kasa daga yankin ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Idan baku manta ba, yankin na Kudu maso Gabas ya fi ba dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi kuri’unsa.
Ina za a kai matsayin shugaban majalisar wakilai?
A taron, shugaban kungiyar ta ‘yan Arewa, Yusuf Amoke ya ce, ya kamata shugabannin APC su mika kujerar shugaban majalisar wakilai ta kasa zuwa Arewa maso Yamma.
Kungiyar ta kafa hujja da cewa, yankin na Arewa maso Yamma ya ba da gudunmawa wajen kawo shugaban kasa mai jiran gado Bola Ahmad Tinubu.
A cewar shugaban kungiyar, la’akari da addini a wajen rabon kujerun shugabancin majalisar zai taimaka matuka wajen damawa da kowa.
Hakazalika, ya ce hakan ne zai nuna tasirin gwamnatin Tinubu wajen tafiya da kowa da kuma tabbatar da ana yin abubuwan da suka dace.
Abdulaziz Yari ya nuna sha’awar gaje kujerar Ahmad Lawal
A wani labarin, kunji yadda tsohon gwamnan jihar Zamfara ya bayyana sha’awarsa ta zama shugaban majalisar dattawa ta kasa.
Ya bayyana hakan ne tare da fadin hujjojinsa na ba yankin Arewa maso Yamma sakamakon kokarin aiki a zaben shugaban kasa na kawo Bola Ahmad Tinubu.
Bayan rantsar da Tinubu a watan Mayu, za a yi rantsar da majalisar tarayya ta 10 a Najeriya don gudanar da aikin shekaru hudu.
Asali: Legit.ng