‘Motar Hedimasta’: Martanin Jama’a Bayan Ganin Wata Balkwatacciyar Motar Malamin Makaranta

‘Motar Hedimasta’: Martanin Jama’a Bayan Ganin Wata Balkwatacciyar Motar Malamin Makaranta

  • Wani matashi ya tsaya a bakin kofar shiga makarantarsu, ya kwatanta motocin da dalibai da lakcarori ke zuwa dasu
  • Ya dauki bidiyon wasu manyan motoci masu kyau da yace dalibai ne ke zuwa dasu cikin makarantar
  • A bangare guda, ya nuna wata motar da ta shigo mai launuka da yawa, inda yace na malami ne, jama’a sun yi martani

Dalibai sun yi nishadi bayan da suka ga wata motar da ta shigo cikin makarantarsu mai launuka da yawa.

Wani dalibi, @richiejay49 ya tsaya daga nesa, inda ya dauki bidiyon dukkan motocin da ke shiga makarantar tare da fadin masu su.

Akalla wasu motoci masu tsada da kyau uku ne suka shigo, inda matashin yace na wasu dalibai irinsa da ke karatu a makarantar ne.

Dalibai sun yiwa malami isgilanci saboda ya zo da wata mota makarannta
Yadda malamin ya shigo da motarsa | Hoto: @richiejay49
Asali: TikTok

Daga gefe guda, wata mota mai launuka biyu ta shigo, inda dalibai suka kwashe da dariya tare da ikrarin cewa, motar ta wani lakcara ne.

Kara karanta wannan

Abin takaici: An kashe malamin addinin Muslunci daidai lokacin buda baki a wata jiha

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jama’a a kafar TikTok sun yi martani, yayin da wadanda suka san mai motar suka caccake shi tare da kiransu sunaye.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a a TikTok

Ga kadan daga abin da mutane ke cewa bayan ganin bidiyon:

@oluyinkaaa:

“Lakcaran da kuka gani a matsakaiciyar motar zai iya sayen duk irin motocin da ka nuna amma ya gwammace ya kashe kudin a wani abu mai amfani.”

@Grace:

"Wannan ba Alayande bane, na san mai motar nan ai.”

@nokutendamutsamba:

"Motar hedimasta kenan.”

@Oluwadamilola:

"Makaranta ta makaranta ta kenan, na san mai motar amma ba zan fada ba.”

@Amicable:

"A makarantarmu ba ka da damar shiga da mota ma..,kuntatawar ta yi yawa ga lakcarori sai suka hana.”

@taofeeqafolabi:

"Wannan ba tsohuwar kwalejin ilimi bane ta Emmanuel Alayande.”

@janewatts19:

Kara karanta wannan

Rayyuka 17 Sun Salwanta A Sabon Rikici Da Ya Barke A Jihar Arewa

"Motar wannan lakcaran ai na da kyau ka zo tsagayar shari’a ka ga mota.”

Budurwa ta ziyarci saurayinta, ya ba ta abinci mai ban mamaki

A wani labarin, kunji yadda wata budurwa ta kai ziyara gidan wani saurayinta, ya hada mata abincin da ya bata mata rai gaba daya.

A cewarta, ya dafa mata doya ba miya, ya dauko manja ya bade sannan ya ba ta ruwan leda yayin da ta isa gidan.

Jama’ar kafar sada zumunta sun yi martani, sun bayyana cewa bata kyauta masa ba, sun yi mata wankin babban bargo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.