Gwamnatin Buhari Ta Caccaki Kasashen Turai da Ke Daukar Nauyin ’Yan Ta’addan IPOB
- Ministan yada labarai da al’adu a Najeriya ya bayyana yadda kasashen waje na Turai ke daukar nauyin ta’addanci musamman na IPOB
- Wannan na zuwa ne a wata tattaunawar da ya yi da masu ruwa da tsaki a kasar Amurka game da zaben 2023 da ya gabata
- Ya yi kira ga a daina yada karya, a kuma yi nazari kafin kafa alkalamin rubutu game da Najeriya, musamman jaridun kasashen waje
Washington DC - Gwamnatin tarayyar Najeriya ta caccaki wasu kasashen yammacin duniya da ke ba kungiyar ta’addancin nan ta IPOB tallafi wajen gudanar da barnarta.
Wannan na fitowa ne daga bakin ministan yada labarai da al’adu, Lai Muhammad a lokacin da yake magana a birnin Washigton DC, Daily Trust ta ruwaito.
A cewar Lai, lamarin tallafawa IPOB ba komai bane face tsagwaron munafunci na yammacin duniya, tare da ikrarin suna yakar ta’addanci, amma a zahiri kara rura wutar rikici suke ta hanyar ba kungiyoyin ta’addanci kamar IPOB kudade.
Lai ya yi bayani dalla-dalla, ya fadi yadda ake tallafawa IPOB
Ministan ya ziyarci Washington DC ne domin tattaunawa da manyan kafafen yada labarai na kasa da kasa game da zaben 2023 da aka kammala.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake jawabi, ya ce:
‘IPOB kungiyar ta’addanci ce haka gwamnatin Najeriya ta ayyana, amma duk da haka wasu kasashen yamma ke ji dasu kuma suke mu’amala da haramtacciyar kungiya.
“Suna ba su damar tara kudi, wasu suna lallabar ‘yan majalisunsu domin tara kudin da idan suka samu suke amfani dasu wajen rutsa kasar.”
Ku daina yada jita-jita game da Najeriya, Lai ga kafafen yada labarai na duniya
Ya kuma yi kira ga kafafen yada labarai na waje da su daina ruruta jita-jita ba tare da fahimtar bayani ba game da zaben Najeriya na 2023 a shafukansu na intanet, rahoton Daily Post.
Ya kuma bayyana cewa, ya kamata su yi tushi da bankado gaskiya kafin wallafa duk abin da suka gani a kafafen sada zumunta.
Obi ya yi martani bayan Lai ya kira shi maci amanar kasa
A wani labarin, kunji yadda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour ya bayyana matsayarsa game da makomar Najeriya.
Peter Obi ya ce, shi ba maci amanar kasa bane, kuma yana mutunta tushe da turbar Najeriya ba tare da neman kawo batanci gareta ba.
A baya Lai Muhammad ya caccaki Obi bayan da wani sauyin murya ya fita na tonon asirin dan takarar na LP game da shirinsa a zaben da ya gabata na shugaban kasa da ‘yan majalisun tarayya.
Asali: Legit.ng