Dan Takarar Gwamnan APC Na Ruwa, 'Yan Sanda Na Neman Sa Ruwa a Jallo

Dan Takarar Gwamnan APC Na Ruwa, 'Yan Sanda Na Neman Sa Ruwa a Jallo

  • Ƴan sanda sun gayyaci ɗan takarar gwamnan APC na jihar Rivers domin amsa tambayoyi
  • Ana zargin ƴan sandan dake tare da ɗan takarar da laifin yin harbi wanda ya halaka wani mutum da jikkata wani daban
  • Rikici dai ya ɓarke tsakanin mambobin APC da PDP a yayin wata zanga-zanga da suka gudanar

Jihar Rivers- Biyo bayan arangamar da akayi tsakanin mambobin jam'iyyar APC da na jam'iyyar PDP, a Fatakwal babban birnin jihar Rivers a ranar Litinin, rundunar ƴan sandan jihar ta gayyaci ɗan takarar gwamnan APC, Tonye Cole, domin amsa tambayoyi.

Kwamishinan ƴan sanda jihar Okon Effiong, shine ya tabbatar da hakan a yayin wata tattaunawa da gidan talbijin Channels Tv a ranar Laraba.

Tonye
Dan Takarar Gwamnan APC Na Ruwa, 'Yan Sanda Na Neman Sa Ruwa a Jallo Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Da yake magana akan wayar tarhon, kwamishinan ya bayyana cewa:

"An gayyaci Tonye Cole ne ya zo tare da hadiman sa waɗanda ƴan sanda ne, saboda zargin da ake masa shine hadimansa sun yi harbi da bindiga inda suka halaka wani mutum."

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Shiga Cikin Jihar Kano, Sun Yi Garkuwa da Matar Wani Basarake da Ɗansa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kuma yi ƙarin haske kan cewa sun kuma gayyaci wasu mambobin jam'iyyar PDP akan irin zargin da ake yiwa Cole. Rahoton Within Nigeria

"A ɗaya ɓangaren kuma, shugaban ƙaramar hukumar Ikwerre, mataimakin kakakin majalisar dokojin jiha da kuma shugaban PHALGA, an gayyace su domin taimakawa ƴan sanda da bincike."

Mambobin PDP da APC sun yi arangama a ranar Litinin yayin da ƴan PDP suka hana Cole shiga ofishin hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) a jihar domin duba takardun sakamakon zaɓe.

Da ak tambaye sa ko da gaske an samu asarar rai a wajen, kwamishinan ƴan sandan sai ya kada baki yace:

“Muna gudanar da bincike, zargin da ake shine an harbi mutum biyu, ɗaya ya rasu amma yanzu mun haƙiƙance sai sun nuna mana gawar wanda ya mutu, kafin nan ba zamu iya tabbatar da cewa wani ya mutu ba."

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Bayyana, Dan Takarar Gwamnan APC Ya Tono Kulla-Kullar Da Ake Shirya Masa Don Hana Shi Zuwa Kotu

"Mun samu damar ganin wanda ya samu rauni, kuma raunin harsashin bindiga ne a ƙafa."

Har ya zuwa yanzu babu ko ɗaya daga cikin Tonye Cole, APC ko PDP da suka ce komai akan wannan lamarin.

Rai Ya Salwanta a Rikicin 'Yan Sanda Da 'Yan Achaba

A wani labarin na daban kuma, an samu tashin hankali tsakanin ƴan sanda da ƴan achaɓa a jihar Legas.

Hargitsin da ya auku ya janyo an samu asarar rai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng